Categories
Taska

Wani Kare ya mutu bayan da wasu mutum hudu sukai masa fyade

Wani kare da aka bayyana sunansa da Courage ya mutu bayan da wasu karti su hudu sukai masa fyade a kasar Indiya.

Jaridar Sun ta kasar Indiya ta ruwaito labarin wannan kare nai nan tausayi. Inda ta ruwaito cewar an garzaya da kare asibiti domin ceton rayuwarsa amma yace ga garinku nan.

Har ya zuwa lokacin da aka hada rahoton ba a kai ya gano wadannan matasa da suka yiwa wannan Namijin kare fyade ba.

Categories
Taska

Yau ake bikin Sallar cika ciki a kasar Amurka

 

Sallar cika ciki a Amurka na iya zama sallar da tafi kowace samar da nishadi, da kuma aiwatar da wasu abubuwa da mutun baiyi suba a duk ilahirin shekarar.

Bukin sallar cika ciki a Amurka ta samo asaline tun a shekrar 1621, kimanin shekaru 397, kenan da aka fara gudanar da wannan bukin, a duk ranar Alhamis ta uku a watan Nuwambar kowace shekara.

Amurkawa kan gudanar da bukin, wanda iyalai kan hadu a ci abinci tare, don yima Allah godiya, da nuna jin dadin su ga Allah da ya basu lafiya da ikon ganin zagayowar ranar.

Sallar na daya daga cikin manya-manyan bukukuwa da ake gudanarwa a kasar Amurka, dangi daga ko’ina suna halartar bukin don ganawa da ‘yan uwa, da saye-saye don bada kyauta ga marasa hali da ma ‘yan uwa da abokan arziki.

Lokacin bukin Amurkawa da ma wasu ‘yan kasashen waje sukanyi amfani da lokacin don yin saye-saye, kaya nayin sauki ga duk mai bukata. Duk gidajen abinci sukan rage kudin abincinsu a wannan rana, don saukakama jama’a.

A lokacin mulkin tsohon shugaban Amurka Abraham Lincoln a shekarar 1863 aka ayyana wannan bukin a matsayin hutun kasa baki daya, itace kuma ranar da ake mata kirari da ranar Talo-Talo, don shine naman da akafi ci sai kuma Alade.

A cewar kungiyar masu saida Talo-Talo ta kasa a shekara da ta gabata an saida Talo-Talo kimanin milliyan 44, a ranar bukin cika cikin, yau da misalin karfe 12:00pm har zuwa tsakiyar dare za ayi ta tande-tande da lashe-lashe a baki dayan kasar Amirka.

 

voahausa.com

Categories
Taska

Ko kun san garin da Rana ba zata fito ba har tsawon kwana 65?

Birnin Barrow dake jihar Alaska ta kasar Amurka, zai fuskanci duhu babu fitowar rana har na tsawon kwanaki 65. Shi dai wannan yanayi ana kiransa da suna Polar Night a turance.

Wannan yanayi na maimaituwa duk shekara a wannan jihar ta kasar Amurka sabida tsananin dusar kankara da take zuba a jihar. Alkaluman kididdiga sun nuna cewar akwai kimanin mutane 4000 dake zaune a wannan yanki da zai yi fama da dare har na tsawon kwanaki 65.

A duk lokacin bazara da tsananin sanyin hunturu irin wannan jihar na fuskantar wannan yanayi na kwanaki 65, kafin daga bisani yanayin garin ya koma yadda yake, da daman mutanan garin dake din ganin Hasken rana kan fita su bar garin a irin wannan lokaci, yayin da wasu mazauna suke zamansu suna ganin ikon Allah.

Lokaci na Karshe da rana ta rufe a wannan gari shi ne ranar Lahadin nan da ta gabata da milasin karfe 1:45, tun daga wannan lokaci ba a kuma ganin rana ba, sai kuma nan da kwanaki 65, sannan yanayin zai dawo yadda yake da na sauran duniya.

Categories
Taska

Dan Najeriya ya lashe gasar cin abinci mai mugun yaji a kasar Chana

Jaridar China Daily ta ruwaito wani dan Najeriya da bata bayyana sunansa ba a matsayin wanda ya lashe gasar cin abinci mai mugun yaji a kasar ta China.

Ita dai wannan gasa mutane daga kasashe biyar ne suka shiga domin gwada sa’arsu ta cinye wani dandakakken nama mai dankaren yajin barkono.

Sai dai kuma dukkab wadan da suka shiga gasar sun gaza cinye abincin yayin da shi dan Najeriya ya cinye ya kuma sude kwanon. An karrama dan Najeriyar da yaci gasar da lambar yabo.

Categories
Taska

Kasar Indiya ta halatta auren jinsi tsakanin ‘Yan Madigo da Luwadi

Kotun koli a Indiya ta halatta yin luwadi da madigo a kasar, matakin da aka dade wasu na adawa da shi.

Kotun ta halarta yin hakan ne ga manya da suka mallaki shekarun girma.

Hukuncin dai ya yi wa masu gwagwarmayar kare ‘yan luwadi da madigo dadi inda suka rungumi juna suna murna bayan zartar da hukunci.

Alkalai biyar ne suka yi nazari game hukuncin da ya yi watsi da hukuncin da ya haramta luwadi da madigo a shekarar 2013 bisa dokar zamanin turawan mulkin mallaka.

Tsohuwar dokar tun zamanin turawan mulkin mallaka da aka fi sani da sashe na 3-7-7 ta zartar da hukuncin duk wanda aka samu da yin madigo da luwadi za a yanke masa hukuncin ko dai sama da shekara 10 a kaso.

A yanzu kotun ta yanke hukuncin cewar nuna wariya bisa game da irin nau’in jima’in mutum toye hakkin dan Adam ne.

Tun da farko ma su fafutuka sun ce ayyana auren jinsi a matsayin laifi, zai zama babbar barazana ga ‘yancin masu ra’ayin auren jinisi daya.

BBCHAUSA.COM

 

 

Categories
Taska

Yadda al’ummar garin Sabuwa ke ratsa Kogi don binne mamata

Daga Yasir Haruna Muhd

Wannan yadda ake kai gawa makabarta kenan a wani kauye da ake kira Sabuwa a Jihar Katsina inda in akayi mutuwa sai an tsallake kogi kafin akai gawa makabarta kamar yadda wani dan’uwa Sadauki dan Ibrahim ya yi korafi sboda rashin hanya sai anbi cimin kogin.

Abin tausayawa musamman a wannan yanayi na damina da muke ciki, ba shakka suna bukatar taimako daga gwamnati musamman ta Jihar Katsina.

Abin lura anan shine:
Yanzu idan ruwa ya cika rafin kenan indai anyi mutuwa sai dai a ajiye gawar har sai ruwa ya ragu yadda za a iya wucewa a kai makabartar ko kuma shikenan sai dai a birne gawan a cikin gari?

Allah Ya sanya wannan kira ta riski wainda alhakin daukan matakin ya rataya a wuyansu, Allah Kuma Ya basu ikon daukar matakin gaggawa.

Categories
Taska

Yadda na jefar da dana saboda na haife shi ba bisa sunna ba

A tsarin rayuwar Bahaushe, babu wani abu da ya fi takaici da kunya irin a ce mace ta yi ciki ba tare da aure ba.

Hakan ce ta sa idan har irin wannan kaddara ta fada wa wasu, sai su yi duk kokarin da za su yi don gujewa haifar cikin.

Halima Umar Saleh, ta ci karo da wata baiwar Allah a birnin Kano, wacce ta fayyace mata labarin wani al’amari da ya faru da ita shekara 12 da suka gabata, na yadda ta yi ciki ba aure ta kuma haifi dan, amma saboda gudun abin kunya sai ta dauki wani mataki da ya sa ta da-na-sani tun ba a je ko ina ba.

Wannan baiwar Allah da muka boye sunanta na gaskiya muka sa mata suna Hariya, ta ce ta tsinci kanta a wani mummunan yanayi yayin da aka wayi gari ta ganta dauke da ciki ba tare da ta yi aure ba.

Hariya mai shekara 35 ta ce tana da shekara 23 ne wani mutum ya yaudare ta ya yi mata ciki, kuma daga baya ya kekasa kasa ya ce cikin ba nasa ba ne.

“Lokacin da na samu cikin na sha wahalar da ban taba tsammanin zan rayu ba, iyayena suka kore ni, sai na koma gidan yayar mahaifina na zauna a can har na haihu.

“Manyana sun so a zubar da cikin don har mun je asibiti, amma sai aka ce ina iya rasa raina sakamakon haka. Wannan tsoron ne ya sa na ce gaskiya abar min cikin kawai.”

Amma da na koma gida sai tunani da damuwa suka shige ni, sai na shaida wa yayar mahaifina cewa na kai yaron nan wani gida amma kuma yanzu na kasa samun nutsuwa.

“Sai muka je don dauko yaron, sai muka samu har an yi cincirindo ana ta ganin dan da kuma jimamin yadda aka jefar da shi,” in ji Hariya.

Ta ci gaba da cewa: “Da kyar suka yarda suka ba mu dan bayan sun ja min kunne kan rashin kamatar abun da na yi.

Rashin aure

Duk da cewa Hariya ta yi da-na sanin abun da ta yi, amma har yanzu shekara 12 bayan hakan ba ta yi aure ba.

Ta alakanta hakan da yadda ake kyamar auren duk wacce ta taba haifar dan da ba na sunna ba a kasar Hausa, duk kuwa da tarin nadamarta.

Sai dai ta ce ita wannan ba ya damunta, a yanzu burinta shi ne ta yi wa danta kyakkyawar tarbiyya ta kuma taimaka wajen ba shi ilimi ta yadda rayuwarsa ba za ta tagayyara ba.

Categories
Taska

Yadda awaki suka mamaye unguwanni a Amurka

Fiye da awaki 100 ne suka mamaye titunan yankin Boise a jihar Idaho da ke kasar Amurka, lamarin da ba a saba gani ba a kasar.

Awakin sun balle ne daga garkensu a ranar juma’a, inda suka shiga gari suna neman abinci.

Awakin sun ja hankalin mazauna Boise inda aka wayi gari da awakin suna kiwo a cikin gari.

An ta yada hutuna da bidiyon awakin a kafafen sada zumunta na Intanet.

Wani a shafin twitter ya ce bayan shekara 30 za su ba jikokinsu labarin yadda awaki suka tsere daga garkensu suka shigo gari.

BBCHAUSA.COM

Categories
Taska

Wasu yara sun makale a karkashin kasa a Thailand

Daga Aminu Ibrahim

Tun daga ranar 23-06-2018 har zuwa yanzu da nike rubutun nan, kai har kilama nanda sati daya ko wata daya ko watanni, babu labari mai ban tausayi da ban al’ajabi daya karade Duniya irin yaran nan ‘yan kwallo ‘yan kasar Thailand wadanda sukabi hanyar karkashin kasa zuwa inda zasuje tareda kocinsu, bayan sunyi nisa a cikin wannan hanya ta kogo akayi wani mamakon ruwan sama ya shigo ya hadu da tabo ya dade hanyar da sukebi gaba da baya!
Yau kwana tara kenan yaran nan ba abinci ba wadataccen iska ga tsananin duhu babu haske, a haka suka zauna cikin jiran mutuwa ta biyosu da taimakon yunwa ta rika daukarsu da dai-dai da dai-dai, amma da yake sunada sauran shan ruwa gaba, mutane gwanayen linkaya daga sassan Duniya sukazo suka zagaye wurin nan, har aka samu wasu gwanayen linkaya ‘yan kasar birtaniya sukayi nasarar isa inda suke bayan sunyi tafiyar kusan KM 4 suka iskesu a raye cikin wani yanayi mai matukar ban tausayi.
Suna ganinsu sukayita murna sun san sunada sauran wata rayuwa a gaba, yanzu dai har anyi nasarar kai masu abinci da magunguna, sauran babban aikin yadda za’ayi hikimar fitar dasu, kasantuwar yarane kanana wadanda shekarunsu suka kama daga 11 zuwa 16 kocinsu kuma mai shekara 25 yanzu dai hasashen masana ya nuna kodai aje a koya masu linkaya, ko kuma aci gaba da aika masu abinci har nanda watan Octorber lokacin ake ganin ruwan zai janye.
Yanzu dai Duniya ta zuba ido taga yadda zaa ceto ran wadannan bayin Allah ba tareda ran ko daya ya salwantaba, Allah yaraba mai rai da wahala.
Categories
Taska

‘Yadda wani malamin jami’ar Bayero ‘ya nemi yin lalata da ni’

A ziyarar da tawagar Adikon Zamani ta kai Jamai’ar Bayero da ke Kano, wasu dalibai mata da maza sun shaida wa BBC yadda wasu baragurbi daga cikin malamansu suke nemansu domin yin lalata da su.

Daya daga cikinsu ta ce “wani malaminmu ya taba cewa yana so na, amma ko da na nuna masa cewa ni ba wannan ne ya kawo ni makaranta ba sai ya yi min barazanar cewa idan dai ban ba shi hadin kai ba, to ni ma lokaci zai zo da zan fado hannunsa.

“Ganin cewa mun yi haka a dole na fasa daukar madda (course) dinsa saboda tsoron kada na fada tarkonsa, kuma Allah ya taimake ni maddar tasa ba ta dole ba ce, don haka kawai sai na ki dauka,” a cewar dalibar wadda ta nemi a sakaya sunanta.

A nata bangaren, Jami’ar Bayero ta ce tana da ka’idoji masu tsauri na tunkarar irin wadannan korafe-korafe.

Shugaban sashin kula da jin dadin dalibai na jami’ar Dr Shamsudden Umar, ya shaida wa BBC cewa makarantar na daya daga cikin wuraren da ba a daurewa irin wannan dabi’a gindi, sannan ya nemi dalibai da kada su ji tsoro wurin bayyana duk wanda ya nemi cin zarafinsu.

Haka shi ma wani dalibi namiji, ya shaida wa BBC yadda ya fada tarkon wani malami kawai saboda yana da alaka da wata daliba da malamin yake nema.

“Lamarin sai da ya kai malamin da abokinsa suka kira ni har ofis suka titsiye ni kan alaka ta da ita saboda suna zargin ta gaya mana cewa yana nemanta bayan da wata kawarta ta kai mai tsegumi.”

Sai da na je kare kaina, amma hakan bai yi wani tasiri ba,” a cewar dalibin wanda shi ma ya nemi a boye sunansa.

Cin zarafi ta hanyar lalata laifi ne a Najeriya, amma duk da haka ana ci gaba da samun aukuwar lamura irin wannan a jami’o’in Najeriya.

A kwanan nan ne wata dalibar Jami’ar Obafemi Awolowo ta tona asirin wani malamin Jami’ar da ya nemi yin lalata da ita.

Dalibar mai suna Monica Osagie ta nadi tattaunawar da ta yi da wani malaminta da ya nemi yin lalata da ita domin ya ba ta damar cin jarabawa tare da watsa tattaunawar.

Lamatrin ya ja hankalin jama’a a ciki da wajen Najeriya.

Dalibar ta Jami’ar Obafemi Awolowo, ta watsa tattaunawar tata ne da Farfesa Richard Akindele, wanda ke koyarwa a sashin harkokin kasuwanci da hada-hadar kudi na jami’ar, a shafukan sada zumunta.

Lamarin dai ya kai ga jami’ar kafa kwamitin bincike wanda a karshe ya sami malamin da laifi kuma aka kore shi daga aiki.

Mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Eyitope Ogunbodede, ya ce an kori Farfesa Richard Akindele ne bayan da ya amsa laifin kulla alaka da daya daga cikin dalibansa ta hanyar da ba ta dace ba.

“Farfesa Akindele ya nemi yin lalata da Monica Osagie domin sauya maki kashi 33 da ta ci zuwa adadin da zai ba ta damar tsallakewa,” a cewar Ogunbodede.

Kusan wannan ne karo na farko da za a iya cewa wata makaranta ta dauki hukunci a bainar jama’a kan irin wannan aika-aika da aka dade ana zargin wasu malaman jami’a da aikata wa.

Kuma babu shakka matakin da Monica ta dauka na tona asirin malamin ya samu karbuwa a wurin daliban jami’a a sassan kasar da ma sauran jama’ar gari, saboda halayya ce da ta dade tana faruwa ba wai a Najeriya kawai ba.

Sai dai a cewar Dr Shamsudden Umar ya ce BUK ta bude wani ofis na musamman mai cin gashin kansa domin bai wa dalibai damar kai korafe-korafe masu kama da irin wadannan.

Ya kara da cewa babu wani malami da za a dagawa kafa idan aka same shi da laifi, yana mai bai wa dalibai kwarin gwiwa domin su bayyana duk wani bara-gurbin malami da suka sani.

BBCHAUSA.COM