Categories
Wasanni

Tottenham ta lallasa Manchester United da ci 3 ba ko daya

Dan wasan Tottenham Lucas Moura me ya zura kwallaye biyu a ragar Manchester United yayin da Hitspour ya zura kwallo daya.

An dai tashi wasan ne Tottenham na da ci uku yayin da ita kuma Manchester take nema, kuma an buga wannan wasan ne a filin wasa na Old Traford na Manchester United.

ya kuke kallon wannan wasan?

Categories
Labarai Wasanni

FIFA ta cire Maradona daga jakadanta sakamakon daga yatsan tsakiya ga ‘yan Najeriya

Hassan Y.A. Malik

FIFA ta yi alwashin daina biyan tsohon dan wasan kwallon kafa na Argentina, Diego Maradona a matsayin jakadanta na kwallon kafa na duniya.

Wannan na zuwa bayan da Maradona ya gaza kimtsa kansa a wasan da kasarsa ta buga da Super eagles ta Nijeriya a ranar Talatar da ta gabata, inda kasarsa ta samu nasara da kyar a kan Super Eagles da ci 2 da 1.

Maradona ya yi murnar zura kwallon Marcos Rojo ta hanyar nunawa magoya bayan Nijeriya dan yatsansa na tsakiya (alamar zagi).

FIFA ta bayyana wannan dabi’a ta Maradona a matsayin abin takaici da rashin nuna kamun kai, inda har ta dauki matakin daina biyansa fam 10,000 da take biyansa a matsayin jakadanta kamar yadda mujallar OwnGoal ta rawaito.

Haka kuma, Maradona ya ki bin umarnin likitocinsa inda suka hana shi kallon karshen wasan domin kare lafiyarsa. Amma sai ya yi kunnen uwar shegu da umarnin na likitoci, dalilin da ya sa ya jefa kansa da kansa cikin haɗarin lafiya

FIFA ta ja kunnen Maradona da ya nutsu ya kuma zama mai kimtsi a ragowar wasannin da kasarsa ta Argentina za ta buga a gasar.
Akwai yiwuwar FIFA ta hana masa sake shiga kallon wasanni in har ya sake maimaita irin abinda ya yi a wasan Nijeriya.

Categories
Wasanni

‘Yan wasan da zasu takawa Najeriya leda a karawar da zata yi da Argentina

Hassan Y.A. Malik

Wata majiya ta cikin gida ta bayyana cewa ocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya, Gernot Rohr ya bayyana cewa zai yi amfani ne da jerin ‘yan wasan da ya yi amfani da su wajen doke tawagar Iceland a wasan da Super Eagles za ta kara da Ajantina a yammacin yau.

A yau din ma dai, Kelechi Iheanacho, Tyronne Ebuehi da Ahmad Musa za su fara, inda Odion Ighalo, Shehu Abdullahi da Alex Iwobi za su zo a benci.

Salon wasan da kocin zai buga shi ne na mutum 3 a baya, 5 a tsakiya, mutum 2 kuma a gaba a matsayin masu zura kwallo.

In ba a manta ba dai, da wannan salo ne Rohr ya yi mafani wajen doke Ajantina a wasan sada zumanta da aka tashi da ci 4 da 2.

A wasan na yau da za a take da karfe 7:00 na yama daidai, Super eagles na bukatar yin nasara akan Ajantina ko akalla ta yi canjaras da Ajantina don samun kaiwa ga zagaye na 16 na gasar cin kofin duniya

Ga jerin ‘yan wasa 11 da Nijeriya za ta fito da su:
Uzohu
Balogun
Ekong
Ebuehi
Idowu
Ndidi
Etebo
Mikel
Musa
Iheanacho
Moses
Categories
Wasanni

Real Madrid za ta wafce Jose Mourinho daga hannun Manchester United

Daga Hassan Y.A. Malik

Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya fara tattaunawa da kungiyar Real Madrid a wani salo na kome zuwa ga kungiyar da ya taba horarwa a baya kamr dai yadda jaridar kwallon kafa ta Ok Diario ta rawaito.

Jaridar ta Ok Diario ta wallafo cewa tuni dai wata tawaga ta Real Madrid din ta tuntubi wakilan Mourinho kan batun ko zai iya barin Manchester United ya koma Real Madrid da aiki.

Wannan kuwa ya bayan gurbin da Zinedine Zidane ya bari ne bayan ya ajiye aiki a wani yanayi na bazato ba tsammani bayan da kungiyar ta lashe gasar cin kofin zakarun turai sau 3 a jere a karkashin kulawarsa.

Mauricio Pochettino, Antonio Conte, Jurgen Klopp, Joachim Low na daga cikin wadanda kungiyar ke hange a matsayin magada ga Zidane, sai dai kwatsam kuma aka jiyo kungiyar ta sanya sunan Mourinho a matsayin wanda kungiyar ke muradin ya jagoranceta.

An ruwaito cewa shugaban hukumar gudanarwar kungiyar, Florentino Perez ne ya bukaci da lalle a nemo Mourinho ya karbi Madrid din wanda dama ya taba rike kungiyar tsakanin shekarar 2010 zuwa 2013.

Dama dai a watan da ya gabata, jaridar Daily Telegraph ta rawaito cewa wasu jiga-jigai a Manchester United sun nuna rashin jin dadinsu kan salon yadda Mourinho ke tafiyar da kungiyar tare da ja masa kunne kan ya canja salonsa a kakar wasa mai zuwa.

A saboda haka, wannan kaka ita ce kaka mafi mahimmaci ga Mourinho a Manchester United, inda zai dada tabbatrwa da wadanda ke da shakku akansa cewa har yanzu fa zai iya canja al’amura.

Tuni dai Mourinho ya kammala daukar ‘yan wasa biyu: Fred daga Shaktar akan fam miliyan 52 da Diogo Dalot daga Porto akan fam miliyan 17.4

 

Categories
Wasanni

Ya kamata a sauya sunan gasar zakarun Turai da suna na – Ronaldo

YAKAMATA A CANJA SUNAN KOFIN ZAKARUN TURAI YA KOMA SUNANA, CEWAR RONALDO

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Cristiano Ronaldo, dan kasar Portugal, ya bayyana cewa ya kamata hukumar kwallon kafa ta nahiyar turai ta canja sunan kofin zakarun turai daga champions league zuwa CR7 champions league.

Ronaldo ya bayyana hakane a hirarsa da manema labarai bayan da kungiyarsa ta Real Madrid ta samu damar lashe kofin karo na 13 a tarihi kuma karo na 3 a jere a hannun kungiyar Liverpool daci 3-1 a kasar Ukraine.

Lokacin da aka tambayi dan wasan cewa ko ya ji haushi da har aka kammala wasan bai zura kwallo a raga ba kuma kungiyarsa ta samu nasara sai yace sam baiji haushi  ba, hasali ma yakamata a canja sunan kofin zuwa sunansa.

Ronaldo ya ce yakamata sunan kofin ya koma sunansa saboda yafi kowanne dan wasa lashe kofin a tarihi sannan kuma ya yafi kowanne dan wasa zura kwallo a raga a tarihin gasar sabida yanada kwallaye 120 kawo yanzu.

A yanzu dai Ronaldo yana bukatar ya lashe kofin sau daya domin ya kamo tsohon dan wasan kungiyar wato Francisco Gento, wanda yataba lashe kofin sau shida a tarihi yanzu kuma yanada guda biyar.

 

Categories
Wasanni

Rashin nasarar Liverpool a wasanmu da madrid, laifi na ne – Karius

Daga Abba Ibrahim Gwale

Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Lucas Karius, dan kasar Jamus ya nemi afuwar kungiyar da magoya bayanta bayan yayi kuskure a kwallaye biyu da kungiyar Real Madrid ta zura a ragar Liverpool a wasan karshen da suka buga ranar Asabar.

kwallo ta farko da mai tsaron yaja aka zura a ragar kungiyar tasa itace ta farko wadda Karim Benzema ya zura a raga sai kuma kwallo ta biyu wadda Bale ya buga daga nesa kuma taje wajen mai tsaron ragar amma kuma yakasa tare kwallon.

Karius yace ranar Asabar ranar bakin ciki ce a rayuwarsa domin shine yasa basu samu nasara ba a wasan sakamkon kura kuran daya tafka kuma yasan kowa baiji dadin abinda yafaru ba musamman magoya bayan kungiyar.

An hango mai tsaron ragar dai yana bawa magoya bayan kungiyar hakuri a filin wasan sakamakon kuskuren nasa kuma wasu daga cikin magoya bayan kungiyar sun amshi hakurin nasa ta hanyar daga masa hannu.

Karius yace yan wasan kungiyar dai basuji dadin abinda yafaru ba amma kuma basu nuna masa ba kawai dai suna bashi hakuri ne suna karfafa masa gwuiwa amma kuma yasan suma basuji dadi ba.

Wannan dai shine karo na 13 da kungiyar ta lashe kofin kuma karo na uku a jere yayinda kuma wannan wasan na karshe shine wanda Liverpool ta buga bayan shekaru 13 batare da tazo wasan karshe ba.

 

Categories
Wasanni

Ramos ya zama dan Rastilin a cewar Klopp

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp ya bayyana cewa dan wasan baya na Real Madrid Sergio Ramos yazama dan risilin kuma fitar Salah ce tasa sukayi rashin nasara akan kungiyarsa.

Kusan za’a iya cewa wasu kwallaye biyu da aka zura a ragar Liverpool laifin mai tsaron ragar kungiyar ne amma kuma ana alakanta rashin nasarar kungiyar da fitar dan wasa Muhammad Salah kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Klopp yace duk da ciwon da Salah yaji yayi kokarin yaci gaba da buga wasan amma kuma ciwon bazai barshi ba kuma dole yafita yana kuka wanda abin bakin cikine ga dan wasan ga Liverpool da kuma kasar Masar.

Mai koyar da kungiya  yaci gaba da cewa Real Madrid tayi kokarin yin amfani da fitar Salah domin su fara kai musu hari amma kuma daga baya sai suka sake nutsuwa bayan da hankalin yan wasan kungiyar ya tashi saboda fitar gwarzon dan wasan.

Sai dai bayan tashi daga wasanne hukumar kula da kwallon kafar kasar Egypt ta bayyana cewa dan wasan buguwa kawai yasamu a kafadarsa kuma suna saran zai samu damar zuwa gasar cin kofin duniya a wata mai kamawa.

 

Categories
Wasanni

Ramas ya yiwa Mo Salah fatan samun sauki

Daga Abba Ibrahim Gwale

Mai koyar da yan wasan  Liverpool Jurgen Klopp ya ce raunin da Salah ya ji a gasar Zakarun Turai ya yi muni sosai, a yayin ake fargabar dan wasan ba zai buga gasar cin kofin duniya ba.

Ko da yake hukumar kwallon kafar Masar na da tabbacin cewa dan wasan zai murmure kafin soma gasar cin kofin duniya da za a fara a 14 ga Yuni.

Salah ya fice fili yana kuka bayan Sergio Ramos yayi masa keta a wasan karshe da Real Madrid ta doke Liverpool 3-1 a babban birnin kasar Ukraine wato Kiev.

Klopp yace”Raunin ya yi muni sosai kuma tuni Salah yana kwance a asibiti za a yi hoton kafadarsa saboda raunin ya yi muni.”

Amma a sakon data wallafa a shafinta na twitter, hukumar kwallon Masar ta ce an yi wa Salah hoto, kuma ya nuna ya samu targade ne a kafadarsa, tare da bayyana cewa tana da tabbacin zai murmure kafin gasar cin kofin duniya.

Salah wanda ya ci wa Liverpool kwallaye 44 a bana, ya yi kokarin ya ci gaba da wasa bayan ketar da Ramos ya yi masa ana minti 26 da fara wasa amma dole daga bisani ya fice fili, inda Adam Lallana ya karbe shi.

Daga baya Ramos ya wallafa sakon fatan alheri ga Salah tare da masa fatan samun sauki, inda ya ce kwallo ta gaji haka.

Salah wanda ya fi yawan cin kwallaye a firimiya ya samu farin jini a kakar bana kuma magoya bayan dan wasan musamman a kasarsa Masar hankalinsu ya tashi, inda suke fatar dan wasan zai murmure da wuri domin jagorantar tawagar kasar a Rasha.

Masar za ta tafi gasar cin kofin duniya a karon farko bayan shekaru 28, kuma ‘yan kasar na ganin Salah zai jagoranci kasar ga nasara.

 

Categories
Wasanni

Cristiano Ronaldo ya bayyana dalilinsa na son barin Real Madrid a bana

Daga Hassan Y.A. Malik

Dan wasan gaba na Real Madrid, Cristiano Ranaldo, na son barin kungiyarsa ta Real Madrid saboda wani dalili nasa na kashin kai da ya dade yana damunsa.

Dalilin na Ronaldo dai bai wuce yadda takwarorinsa na Barcelona Lionel Messi da PSG Neymar Jnr suka fi shi daukar albashi ba.

Kafar Sky Sports ta rawaito cewa, ba wai Ronaldo na cikin wata damuwa bane ko yana da matsala da hukumomi ko abokan wasansa a Real Madrid, a’a! Matsalarsa daya ita ce, shi yana daukar albashin fam dubu 350 a mako, amma Neyamr na daukar fam dubu 600, Messi kuma na daukar fam dubu 750.

Wannan dai na zuwa na bayan da dan wasa  Ronaldo ya yi wani jirwaye mai kamar wanka inda ya bayyana rayuwarsa a Real Madrid a matsayin wani abu da ya gabata.

Ronaldo ya yi wannan batu ne a bayaninsa na bayan wasan karshe na cin kofin zakarun turai da suka buga da kungiyar Liverpool, inda Madrid ta lallasa Liverpool da ci 3 da 1.

Categories
Wasanni

Kungiyoyin kwallon kafa 10 da suka fi daraja a Turai

 

Manchester United – €3.255bn

Real Madrid – €2.92bn

Barcelona – €2.78bn

Bayern Munich – €2.55bn

Manchester City – €2.16bn

Arsenal – €2.10bn

Chelsea – €1.76bn

Liverpool – €1.58bn

Juventus – €1.30bn

Tottenham – €1.29bn

Mista Sartori ya kara da cewa: “Daya daga cikin dalilan da suka kawo wannan karin shi ne tasirin kungiyoyin Ingila da kuma karin tattalin arzikin wasu matsakaitun kungiyoyin da aka yi nazari akansu, wanda ke nuna biyayya ga dokar hukumar Uefa kan adalci kan kudi.”

Duk da cewa kungiyoyin Ingila ne suka fi yawa a cikin 10 na farko, akwai qarin wasu kungiyoyin Ingila uku- West Ham United da Leicester City da kuma Everton – cikin qungiyoyi 20 da suka fi daraja.