uban Amarya Charley Boy

Fitaccen mawakin nan da aka fi sani da Charles Oputa ko kuma Charlyboy a ranar Asabar ya bayar da auren ‘yarsa ta fari Adaeza Oputa ga Metu Anu dukkansu daga jihar Imo.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ta ruwaito cewar an gudanar da auren ne bisa al’adun gargajiya a unguwar gwarinpa dake babban birnin tarayya Abuja.

An gudanar da bikin da kasaitacciyar liyafa a wajen yin hidindimu na Everlyn inda fitattun mawaka da makada daga masana’antar shirya finafinai ta Najeriya.

Manyan jami’an Gwamnati da dama ne suka halarci wannan kasaitaccen biki ciki kuwa harda tsohuwar ministar Ilimi Oby Ezekwesili.

Fitattun ‘yan wasan kwaikwayon kudancin Najeriya da suka hada da Francis Duru da Nkem Owoh suna daga cikin wadan da suka nishadantar a wajen bikin.

A lokacin da NAN ta tattauna da uban amarya CharlyBoy ya nuna jin dadinsa ga wannan aure, ya kuma yiwa ma’aurantan fatan alheri.

“Abun farnciki ne kwarai da gaske ga kowane uba yaga ya aurar da ‘yarsa, ina kuma yi musu murna da fatan Allah ya basu zaman lafiya”

“Ina mai basu shawara da su gina rayuwar aure mai inganci tare da soyayya da kuma kaunar juna a matsayinsu na mata da miji” A cewar uban amarya CharlyBoy.