
Cibiyar Nazari da Bincike kan Cin-hanci ta Ƙasa, CIFCFEN, ta baiwa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari lambar yabo a kan ƙwazo wajen yaƙi da cin-hanci da rashawa a ƙasar nan.
CIFCFEN ta ce ta yi la’akari ne da jajircewar Buhari a tsawon rayuwarsa wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma sadaukar da kai da gaskiya.
Shugaban kwamitin gudanarwa na kwamitin amintattu na CIFCFEN, Dakta Iliyasu Gashinbaki, ne ya bai wa shugaban ƙasar lambar yabon a jiya Talata a Abuja.
Kyautar ita ce babbar lambar yabo ta Cibiyar da aka keɓe ga shugabannin ƙasashen Afirka kawai waɗanda ke da nagarta da halaye nagari.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar, shugaban na Nijeriya shi ne shugaban Afrika na farko da aka baiwa kyautar.
Da yake karɓar lambar yabon, inji Adesina Buhari ya gode wa CIFCFEN, inda ya nuna farinci cikin sa, inda ya ƙara da cewa lambar yabon ta ƙara masa ƙarfin gwiwa da kuma imani cewa yana yin abinda ya dace
Shugaban ya kuma yi alƙawarin duba da kuma amince wa da dokar da ke neman kafa CIFCFEN a hukumance, yana mai cewa kudurin yana gabansa a halin yanzu.
Ya yabawa Cibiyar da ke aiki yadda ya dace da kokarin hukumomin tabbatar da doka da suka hada da Hukumar Yaki da cin Hanci da Rashawa, EFCC, Hukumar ICPC da Hukumar Da’ar ma’aikata, CCB, da kuma ‘Yan sanda.
Ya kuma umurci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da su ci gaba da hada hannu da Cibiyar domin amfanin kasa.