Home Labarai CIKAKKEN BAYANI: An samu Daso a mace bayan ta ɗauki azumin yau

CIKAKKEN BAYANI: An samu Daso a mace bayan ta ɗauki azumin yau

0
CIKAKKEN BAYANI: An samu Daso a mace bayan ta ɗauki azumin yau

An samu fitacciyar ƴar fim din Hausa na Kannywood, Saratu Gidado, wacce aka fi sani da Daso a mace bayan ta dauki azumin yau Talata.

Daily Trust ta rawaito cewa dangin marigayiyar sun shaida wa Freedom Radio rasuwar tata bayan an same ta a mace da safe a yau Talata.

Ƴan uwan na ta sun ce an same ta a mace bayan ta koma barci Bayan ta yi sahur din azumin Ramadan na 30 a yau da safe.

An haifi Daso a ranar 17 ga watan Janairu, 1968 a jihar Kano.

Ta fara harkar fim a 2000, inda ta yi suna a ɓangaren barkwanci kuma fim din ta na farko shine Linzami na Wuta da kamfanin Sarauniya Movies.

Daily Nigerian Hausa na addu’ar Allah Ya jikan ta da Rahma, Ya baiwa iyalin ta hakurin rashin ta, ameen