
Mako daya da dawowa daga ziyarar da ya kai kasar Faransa, shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin tafiya kasar China.
Daily Trust ta rawaito cewar Ajuri Ngelale, mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, ziyarar ta kasar Sin za ta gudana ne a makon farko na watan Satumba.
Ngelale ya ce, hulda da kasar Sin wani bangare ne na kokarin da gwamnatin Tinubu ke yi na inganta rayuwar ƴan Najeriya.
A kasar ta China, ana sa ran Tinubu zai gana da shugaban kasar Sin Xi Jinping, inda za a rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU).
Shugaba Tinubu zai kuma gana da manyan jami’an kamfanoni goma a kasar Sin a fannonin mai da iskar gas, samar da Aluminum, Noma da fasahar tauraron dan adam.