Home Labarai Daga yau kar a sake samun jinkirin biyan albashin sojoji – Matawalle ya bada umarni

Daga yau kar a sake samun jinkirin biyan albashin sojoji – Matawalle ya bada umarni

0
Daga yau kar a sake samun jinkirin biyan albashin sojoji – Matawalle ya bada umarni

Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi kira da a rika gaggauta biyan sojoji albashinsu.

Ya ce rundunar sojin kasar na sadaukarwa sosai don ganin an tabbatar da zaman lafiya a kasar, don haka akwai bukatar a rika biyan su cikin gaggawa.

Mista Matawalle ya bayyana haka ne bayan ya shiga tsakani wajen biyan albashin watan Disamba ga sojoji, wanda tun da fari aka samu jinkiri daga hukumomin da abin ya shafa.

Daraktan yada labarai da hulda da jama’a a ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a jiya Litinin.

Ya ce Mista Matawalle ya sahidawa Akanta Janar na Tarayya da Babban Bankin Najeriya, CBN, domin gaggauta warware matsalar biyan albashin.

Ya ce: “Shiga maganar da Ministan ya yi ya zo ne a kan rashin biyan albashin watan Disamba ga sojojinmu na Najeriya a wannan lokacin bukukuwa.

“Ganin yadda lamarin ke da matukar muhimmanci, Mista Matawalle da kan sa ya yi duk wata tuntuba ga hukumomin da ke kula da biyan albashi, kuma a yanzu jami’an sojojin mu na iya yin farin ciki biki tare da ‘yan uwansu saboda albashin su ya fara fadawa a asusunsu.