21.1 C
Abuja
Tuesday, February 7, 2023

Na daina amfani da ‘Social Media’ sabo da ta na bani hawan jini — Tinubu

Must read

Dan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya ce kafafen sada zumunta, wato social media na saka mishi hawan jini.

A wani fefen bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta a yau Asabar, an nuna Tinubu na cewa ya dena amfani da ‘social media.

Tinubu ya ce ya lura da yadda a ke cin mutuncinsa a kafafen sadarwa kuma a cewar sa, hakan na ɓata masa rai matuƙa.

“Tuni na dena social media sabo da zagin da a ke mini ya yi yawa,” a cewar Tinubu a bidiyon wa ce ba ta da kwanan watan da a ka ɗauka.

“Idan ina karanta irin zagin da a ke yi min, sai jini na ya riƙa hawa. Shi ya sa na deba karanta wa. Idan ina son jin wani abu, to ƴaƴa na ko ma’aikata na sa riƙa gaya min cewa wane ya ce kaza, wane ya ce kaza. Idan kuma abin ya ishe ni, kawai sai na ce da Allah ku manta da shi,” in ji Tinubu.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article

- Website Designed By DEBORIAN.COM, a Nigerian Web Designer and Web Developer -