
Dakarun Isira’ila sun kutsa kai cikin asibitin Al Shifa, asibiti mafi girma a Gaza, inda ganau suka ce sun rika bincike dakuna da kasan ginin, lamarin da ya haifar da damuwa bisa halin kananan yara da jarirai da dubban farar hula da suka samu mafaka a ciki.
Asibitin Al Shifa da ke kwaryar garin Gaza ya kasance wajen da dakarun Isira’ila suka kafawa kahon zuka, inda su ke cewa nan ne gurin da mayakan Hamas ke haɗa makamai suna kai wa Isira’ila hari a kasan ginin asibitin.
Hankalin duniya ya yi kan mutane daruruwa da ke cikin asibitin su ke neman mafaka ba tare da wutar lantarki da kayan agaji ba.
Mahukunta na Gaza sun ce Mutane da dama, da suka hada da jarirai yan watanni uku-uku sun rasu a kwanakin nan sakamakon tsinke da dakarun Isira’ila su ka yi wa asibitin.
Sai dai kuma Isira’ila ta ce dakarun nata sun kashe matakan Hamas a wajen asibitin a yayin wani harbe-harbe da ya barke, inda ta ce sun kashe ƴan Hamas ɗin da dama kuma dakarun nata sun shiga da kayan agaji da magunguna cikin asibitin.