Home Labarai Dakataccen shugaban jam’iyyar PDP a Ondo ya rasu

Dakataccen shugaban jam’iyyar PDP a Ondo ya rasu

0
Dakataccen shugaban jam’iyyar PDP a Ondo ya rasu

Allah Ya yi wa dakataccen shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Ondo, Fatai Adams rasuwa.

Adams ya rasu ne a jiya Talata da daddare bayan ya yi korafin yana jin ciwon kai a gidan sa na saukar baki a Ikare Akoko.

Daily Trust ta jiyo cewa an rankaya da Adams zuwa asibiti, amma daga bisani ya ce ga garinku nan.

A ranar 2 ga watan Janairu ne shugabancin PDP na jiha ya dakatar da marigayi Adam bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa.