Home Labarai Dalibar jami’a ta ɓata a kan hanyarta ta zuwa makaranta a Kogi

Dalibar jami’a ta ɓata a kan hanyarta ta zuwa makaranta a Kogi

0
Dalibar jami’a ta ɓata a kan hanyarta ta zuwa makaranta a Kogi

Wata ɗaliba ƴar aji 2 a Jami’ar Tarayya da ke Lokoja, jihar Kogi, mai suna Janet Kyeme ta ɓata a kan hanyarta ta zuwa jami’ar.

Ba a dai bayyana ko lamarin da ya faru da sanyin safiyar Juma’a a kan hanyarta ta zuwa babbar harabar jami’ar da ke Felele a Lokoja na da alaka da yin garkuwa da mutane ba.

Jaridar Daily Trust, ɓangaren City & Crime ta tattaro cewa ganin ƙarshe da aka yi wa Janet, dalibar Sashen Ilimin Laburare da Kimiyyar Labarai (LIS) shine da safiyar Juma’a lokacin da ta dauki babur din haya daga gidansu da ke barikin sojoji na Zango a Lokoja a kan hanyarta ta zuwa makarantar.

Mai riƙon dalibar, limamin cocin Pentecostal da ke Lokoja ne ya baiyana batan nata lokacin da aka fuskanci lokaci ya kure ba ta dawo daga makaranta ba a wannan rana.

“Da sanyin safiyar Juma’a ta tafi makaranta kamar yadda ta saba. A ranar ba ta dawo daga makaranta ba, wanda ke riƙon ta, wanda Fasto ne da sauran ƴan uwa sun nemi wayar amma a kashe.

“An tura wata ’yar’uwa makarantar don tabbatar da inda take amma ba a sake ta ba. Gana daga hankalin su ya tashi saboda ba a ganta ba kuma babu wanda ya tuntube su a kan ta,” in ji Fasto Joseph, wani makusancin dangin.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO), SP William Aya, ya ce ga dukkan alamu dai ta ɓata ne a halin yanzu tunda idan ɗauke ta aka yi, masu garkuwar da ita basu tuntubi dangin ta ba.