
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware kashi 30 cikin 100 na kasafin kudi na 2024 ga ilimi domin sake farfado da fannin domin ci gaban zamantakewa da tattalin arziki mai dorewa.
Yusuf ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da wasu ayyuka a Jami’ar Bayero, BUK.
Ya ce ayyukan da aka samar a jami’ar za su inganta harkar koyo, bincike da kuma fadada ingancin ilimin jami’a, inda ya kara da cewa wannan karimcin na nuna babban yunkuri na inganta fannin binciken likitanci a jihar.
Gwamnan ya ce gwamnati ta taimaka wa dalibai marasa galihu da kuma rage kudin makaranta da kashi 50 cikin 100 a duk manyan makarantun jihar.
“Za mu ci gaba da kulla alaka da shugabancin Jami’ar da sauran manyan makarantun jihar. Jami’ar Bayero za ta kasance daya daga cikin nasarorin da aka samu a jihar,” inji shi.
Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Abbas ya ce Gwamnatin jihar ta biya wa sama da dalibai 6,000 kudin makaranta, inda ta kara da cewa shi ne mafi yawan kudaden da aka biya kawo yanzu,” inji shi.
Abbas ya ce jami’ar za ta ci gaba da hada kai da gwamnatin jihar domin samun nagartar ilimi.