Home Labarai Dalilin da ya sa muka hana wasu ƴan Nijeriya shiga ƙasar mu — Saudiyya

Dalilin da ya sa muka hana wasu ƴan Nijeriya shiga ƙasar mu — Saudiyya

0
Dalilin da ya sa muka hana wasu ƴan Nijeriya shiga ƙasar mu — Saudiyya

Ofishin jakadancin Saudiyya a Najeriya ya yi ƙarin haske kan rahotonnin mayar da ‘yan Najeriya 264 a lokacin da suka shiga ƙasar, yana mai cewa ba da wata manufa aka yi hakan ba.

A ranar Litinin ne gwamnatin Saudiyya ta soke bizar wasu fasinjoji da jirgin Air Peace ya ɗauka a lokacin da suka sauka a ƙasar bayan tashin su daga Kano – abin da ya sa ƙasar ta buƙaci fasinjojin su koma Najeriya.

Cikin wata sanarwar da ofishin jakadancin Saudiyyar ya fitar ranar Laraba, ya ce “fasinjojin da aka hana shiga ƙasar, ba su cika sharuɗɗa da dokokin Saudiyya ba, saboda sun gabatar da bayanan da ba na gaskiya ba domin samun bizar da ba ita ya kamata a ba su ba, inda sai bayan sun isa Saudiyya ne aka gano hakan”.

Sanarwar ta ƙara da cewa ”Ba ‘yan Najeriya kaɗai aka yi wa hakan ba, har da na wasu ƙasashe”.

Haka kuma ita ma ma’aikatar harkokin ƙasashen waje ta Najeriya cikin tata sanarwar da ta fitar ranar Talata, ta ce ‘tana bincike game da lamarin, domin tabbatar da ko an saɓa wata ƙa’ida”.

Mataimaki na musamman ga ministan harkokin wajen ƙasar, kan kafofin yaɗa labarai, ya ce ma’aikatar za ta tabbatar da irin wannan abu bai sake faruwa kan ‘yan ƙasar ba a nan gaba.

Ofishin jakadancin na Saudiyya ya kuma fitar da gargaɗi ga mutanen kan su riƙa cika ƙa’ida wajen neman bizar shiga ƙasar.

”Haka kuma muna son jaddada muhimmancin bin ƙa’idoji da dokokin da saudiyya ta gindaya ga duka mutanen da ke da burin zuwa kasar”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Daga ƙarshen ofishin ya buƙaci duka fasinjojin da ke muradin ziyartar ƙasar da su riƙa nazarin takardun bizarsu, domin dacewa da dokokin ƙasar kafin su fice daga ƙasashensu zuwa Saudiyya.”

BBC Hausa