Wani dan yawon bude ido dan asalin kasar Sin ya kwankwade jarkar madararsa bayan da jami’an iyafit din kasar AUSTERALIYA suka hana shi shigewa da ita zuwa kasar.

A cewar jami’an fulin jirgin saman, madarar tayi yawan da ba za a barshi ya shige da ita ba, shi kuma dan chana a madadin yayi asara ya zauna ya kwankwade jarkar madararsa gaba daya.