
Ƴan Najeriya da dama sun kaɗu bayan dan jarida mai binciken kwakwaf, David Hundeyin ya fallasa cewa an nemi a bashi toshiyar baki don yi wa matatar mai ta Dangote ƙage.
Hundeyin, ya bayyana yadda wata ƙungiya mai zaman kanta ta kasa da kasa ta yi masa tayin kudi dalar Amurka dubu 800 domin ɓata suna ga matatar mai ta Dangote.
Matatar man dai za ta iya tace ganga dubu 650 na ɗanyen mai a kullum.
Ɗan jarida Hundeyin, a wasu bayanai da ya wallafa daban-daban a shafin X, yayi bayanin cewa ya yanke shawarar bayyana lamarin ne domin aika sako ga wadanda ke kokarin kawo nakasu ga matatar wacce zata taimaki sama da mutane Miliyan 500 na ƙasashen Afrika ta yamma.
Da yake bayyana ra’ayinsa kan kalaman dan jaridar, Henry Adigun, mai sharhi kan al’amuran da suka shafi makamashi ya ce yasan dan jaridar kuma ya aminta da labarinsa.
Adigun, ya ce abu ne mai yiwuwa a tunkare shi da wannan batu sannan ya bayyana farin cikinsa kan karfin gwiwar da ya nuna wajen bayyana al’amarin.
Shima da yake bayyana nasa ra’ayin, Shugaban kungiyar yan jaridu ta JOEDER, Wale Adeoye ya ce bayanan sun nuna yadda ake nuna rashin imani a kasuwar tattalin arziki da kuma nufin durkushe kasashe.
Matatar man ta Dangote dai na fuskanta barazanar fara aiki inda take zargin kamfanin mai na kasa NNPCL ya gaza wajen bata wadataccen danyen mai.
Leadership