Home Labarai Dan Majalisar Tarayya na Fagge, MB Shehu, ya raba N5m ga magoya bayansa a Kano

Dan Majalisar Tarayya na Fagge, MB Shehu, ya raba N5m ga magoya bayansa a Kano

0
Dan Majalisar Tarayya na Fagge, MB Shehu, ya raba N5m ga magoya bayansa a Kano

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Fagge a jihar Kano, Muhammad Bello Shehu ya raba Naira miliyan biyar ga magoya bayansa na jam’iyyar NNPP a jihar Kano.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa mutane 43 ne daga mazabar Yanmata Gabas da Fagge A su ka amfana da tagomashin.

Da ya ke jawabi a wajen rabon kuɗin, dan majalisar, wanda aka fi sani da MB Shehu, ya ce ya yi rabon ne a matsayin ramakon biki sakamakon gudunmawar da su ka bashi a yayin yakin zaɓen sa.

A cewar sa, wadanda su ka ci gajiyar, za su yi amfani da kudin me wajen kara jari a sana’o’insu, ko kuma marasa sana’a, su yi amfani da kudin a matsayin jari.

Ya yi bayanin cewa mutane 16 daga ciki za su amfana da Naira dubu 200 kowannen su, inda 7 daga cikinsu kowa zai samu Naira dubu 100, sai kuma mutane 20 kowanne za a bashi Naira dubu 50.

MB Shehu ya ce zai ci gaba da rabon kuɗin, wanda daga cikin albashin sa ne, a duk wata, inda ya ce zai rika baiwa ƴan jam’iyya a mazabu biyu duk wata har zuwa watan Disamba na 2024.

Ya kuma shaidawa al’ummar Fagge da su sha kurumin su don ya tanadar musu kaɓakin arziki na aiyukan more rayuwa a lungu da sako tare da talkafawa tattalin arzikin al’umma.