Wakilin Najeriya a gasar karatun Qurani a birnin Makkah

Ranar laraba ne aka kammala musabakar karatun Qurani mai girma ta duniya da aka yi a birnin Makkah mai tsarki. Inda mutane daban daban daga sassan kasashen duniya suka halarci gasar.

Faisal Muhammad Auwal daga jihar Zamfara shi ne ya wakilci Najeiya a gasar karatun Quranin a matakin izufi 60 da Tafseer. Faisal ya samu nasarar zamowa na biyu a matakin duniya baki daya.

Sannan kuma, shima wani dan Najeriya mai suna Albashir Goni Usman daga jihar Borno yaci nasarar zuwa mataki na biyu a izufi 60 babu Tafseer. Wadannan sune mutum biyu da suka wakilci Najeriya a wannan gasa da ake yi duk shekara a birnin Makkah.

Najeriya dai na samun halartar shiga wannan gasa da ake gudanarwa a duk shekara a birnin na Makkah mai tsarki. Tuni dai aka raba kyaututtuka ga wadan da suka yi nasara a wannan gasa, wanda babban limamin masallacin Ka’aba Sheikh Abdul-Rahman Sudais ya jagoranci rabawa.