Lamarin dai ya faru ne da sanyin safiyar a Alhamis, idan Shugaban hukumar kwana kwana ta jihar Kano yace sun samu kiran gaggawa daga wani Mohammed Musa cewar gina ya rufta da wani magidanci a unguwar kofar Naisa.

Lamarin dai ya faru ne a tsakiyar unguwar kofar Naisa dake yankin karamar hukumar Gwale, inda gina ya ruguje akan wani magidanci mai suna Muhammad Zakiru, inda cikin ikon Allah aka kubutar da shi.

Haka kuma, shugaban hukumar ta kwana kwana ya yi kira ga Jama’a musamman wadan da ke zaune a gidajen kasa da su guji zama a cikin irin wadannan gidaje musamman a wannan lokaci na damina.