Home Labarai TY Danjuma Ya ƙaddamar da cibiyar fassara ‘Bible’ zuwa yaren Jukun a Taraba

TY Danjuma Ya ƙaddamar da cibiyar fassara ‘Bible’ zuwa yaren Jukun a Taraba

0
TY Danjuma Ya ƙaddamar da cibiyar fassara ‘Bible’ zuwa yaren Jukun a Taraba

 

 

Janar Theophilus Danjuma mai ritaya ya ƙaddamar da Cibiyar Ilimin ‘Bible’ da Yaren Jukun a Ƙaramar Hukumar Takum da ke Jihar Taraba.

Ya ce an kafa cibiyar ne domin bunƙasa fassarar littafin ‘Bible’ da yaren Jukun.

Danjuma Ya ce aikin fassarar ya samo asali ne tun lokacin wata baturiya ƴar Amurka, Margrete Dykestra, da taimakon wani ɗan Nijeriya, Joel Omiri.

Ya ƙara da cewa kafin ta koma gida Amurka, Dykestra ta danƙa mishi gaba ɗaya kundin fassarar littafin mai tsarki, in da ta roƙe shi da ya ƙarasa aikin.

Danjuma ya kuma yi kira ga al’ummar Jukun da su daure su yi amfani da ‘Bible’ ɗin na fassarar Jukun wajen yaɗa koyarwar addinin Kiristanci da kuma samar da zaman lafiya tsakanin al’umma a yankin na su.

Ya kuma shawarci al’ummar da su yi amfani da wannan dama wajen ganin cewa Yaren na Jukun ya ci gaba da bunƙasa, ba wai ya ƙare ba.

Ya ce ba za ta yiwu a ci gaba da koyawa ƴaƴa Yaren turanci ba, inda ya ce har kunya ya ke ji idan ya na yi wa ƴaƴan sa turanci.

Ya kuma ce fassara ‘Bible’ ɗin da Yaren Jukun ba ya na nufin su ka haɗa da wata coci ba ne, inda ya ce a na amfani da damar ne wajen yaɗa addinin Kirista da yaren gargajiya.