
Wani mutum da bidiyonsa ta karade shafin Tiktok ya na tallan cincin cikin raha da ban dariya ya samu gayyata daga fitaccen mawakin nan Davido.
Mutumin dai ya yi fice a shafin Tiktok, inda ake hango shi dauke da robarsa ta tallan cincin kuma ya ke tallansa cikin raha.
Sai dai kuma da rabi ya zo wa mai tallan, sai mawaki Davido ya gayyace shi, inda ya nemi ya kawo masa cincin din kuma zai sayi duk guda ɗaya kan Naira dubu 500.
” Ina son mutanen da suke kasuwancinsu da salo. Zabi biyu ne ko ka jajirce ko kuma ka juri zaman gida. Dan uwa ya jajirce, yanzu ne lokacin da za a tallafa masa”, – Inji Davido.