
Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, ICPC, Musa Aliyu, SAN, ya gana da wakilin DAILY NIGERIAN, Umar Audu, wanda ya fallasa yadda ake bada shaidar digiri na bogi da jami’o’in marasa inganci ke yi a Benin da Togo.
A cikin wani rahoto da DAILY NIGERIAN ta buga a ranar 30 ga watan Disamba, jaridar ta fallasa yadda wasu ɓatagari a jami’an gwamnati ke taimaka wa damfara wajen bada shaidar kwin digiri.
Yayin ganawa da wakilin jaridar DAILY NIGERIAN, ICPC ta nemi wasu bayanai daga dan jaridar domin baiwa hukumar yaki da cin hanci da rashawa damar gudanar da bincike kan badakalar ilimi.
“Don tantance cikakkun bayanai domin kaucewa shakku, shugaban ICPC Dr. Musa Adamu Aliyu, SAN, ya kira wani muhimmin taro a yau a hedkwatar ICPC da ke Abuja tare da wani dan jarida daga kafar yada labarai,” in ji wata sanarwa da kakakin ICPC, Azuka Ogugua ya fitar.
“Sun tattauna kan rahoton da aka fitar ranar 30 ga Disamba kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi a jami’ar Cotonou, da nufin zurfafa bincike da fara aiwatar da ayyukan da suka dace.
A jiya Talata ne dai Ma’aikatar Ilimi ta Ƙasa, a wata sanarwa da Augustina Obilor-Duru ta sanyawa hannu, ta sanar da dakatar da karɓar digiri daga Kwatano da Togo.