24.3 C
Abuja
Saturday, January 29, 2022

Direbobin Adaidaita-sahu sun tsunduma yajin aiki a Kano

Must read

Direbobin babur mai ƙafa uku, wanda a ka fi sani da adaidaita-sahu a Jihar Kano sun tsunduma yajin aikin gargaɗi na mako ɗaya da ga yau Litinin.
Tun a ranar 30 ga watan Disambar da ya gabata ne ƴan adaidaita-sahun su ka yi barazanar tsunduma yajin aiki.
Matakin na su ya biyo bayan ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana da suke yi bisa umarnin sauya lambar babur ɗin da hukumar KAROTA ta ba su inda su ka yi zanga-zanga ta lumana a jihar.
Zanga-zangar dai ta biyo bayan yadda hukumar KAROTA ta ce sai sun biya kudi Naira 8,000 domin sabunta lambar ta su.
Sun kuma koka kan yadda KAROTA ke karɓar kuɗaɗen haraji barkatai a hannun su, musamman ma naira 100 da su ke biya kullum.
A cewar su, ba biyan naira 100 ɗin ne ke damun su ba, wacce su ke biya ta ranar lahadi, duk da cewa jami’an karɓar harajin ba sa fita aiki a ranar, amma a washegari Litinin sai a ce sai su biya har da ta ranar Lahadin.
“Kuma fa har yanzu ba a bamu na’urar nan ta ganin inda mai adaidaita-sahu ya ke ba, duk da cewa mun biya kuɗin tun sama da shekara ɗaya.
“Kullum sai an karbi kuɗaɗe a hannun mu kuma ba ma ganin amfanin kuɗin da mu ke biya,” in ji wani direban adaidaita-sahu.
Da ga ƙarshe, matuƙa baburan sun baiyana cewa da ga lokacin da hukumar KAROTA ta fara kamasu, su ma za su tafi yajin aiki.
Daily Nigerian Hausa ta gano cewa tun a jiya dai matuƙa baburan su ka raba sanarwar tafiya yajin aikin, duk da cewa takardar sanarwar ba ta ɗauke da sa hannun kowa, inda su ka umarci matuƙa adaidaita-sahu da su zauna a gida, su ka kuma yi barazanar kama babur ɗin masu kunnen ƙashi a cikin su.
Sai dai kuma tun a jiyan, jaridar nan ta gano cewa da yawa da ga matuƙa baburan adaidaita-sahun sun fara saka ganye a jikin baburan na su, inda hakan ke nufin shirye-shiryen tsunduma yakin aiki a yau.
A tuna cewa tun a farko-farkon shekarar da mu ke bankwana da ita ne matuƙa baburan adaidaita-sahu su ka tafi yajin aiki sakamakon harajin naira 100 da a ka sanya musu a kullum, inda hakan ya kawo naƙasu a kan al’amuran yau da kullum a jihar.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Latest article