
Rundunar ƴansandan Najeriya, reshen jihar Kano ta tabbatar da kama riƙaƙƙun yan daga 22 da sara da sukan al’umma a unguwar Ɗorayi da ke jihar.
Matakin ya zo ne sakamakon ɓarkewar faɗa tsakanin ƴan daba a unguwar a jiya Laraba, sanadin da ya kauye ya koma kai harin kan me uwa da wabi, musamman ga Musulmai da ke dawowa daga sallar Asham.
A wani taron gaggawa da masu ruwa da tsaki da Kwamishinan Ƴansanda na jihar, Muhammad Usaini Gumel ya kira a yau Alhamis, ya bayyana cewa rundunar ta kuma ayyana neman wasu yan daba 30 ruwa a jallo. Ya ce yan daga ne da ake zargi da suka addabi Ɗorayi da ke ƙaramar hukumar Gwale.
A cewar Kwamishinan, duk wani uba da ya zo belin dansa to za a rike shi a matsayin abokin aikata laifin nasa.
Muhammad Usaini Gumel ya kuma bayyana aniyar rundunar ta samar da sabon ofishin yaƙi da ayyukan daba a unguwar ta Ɗorayi.