
Gwamnatin tarayya, karkashin shugabancin kasa Bola Ahmed Tinubu, ta kashe naira biliyan 2.3 wajen tafiye-tafiyen kasashen waje da kuma sauran saye-saye a cikin watanni shida, kamar yadda bayanai daga GovSpend, wani rumbun bayanai da ke tattara bayanan kudaden da fadar shugaban kasa ke kashe wa.
Daily Trust ta rawaito cewa wannan ya nuna irin kudaden da aka kashe wajen tafiye-tafiyen shugaban kasa tsakanin ranar 21 ga watan Fabrairu zuwa 19 ga watan Yuli na wannan shekara.
Hedikwatar fadar gwamnati da ke Abuja, a lokacin, ta tattara bayanan kudaden tafiye-tafiyen shugaban kasa, daga Naira miliyan 300 a ranar 21 ga Fabrairu, 2024, na saye-sayen watan Janairu.
“A ranar 24 ga Fabrairu, Majalisar Dokokin Jihar ta kuma biya Naira miliyan 250 na tafiye-tafiyen Shugaban kasa da kuma abubuwan da suka dace. Kuma a ranar 15 ga Maris, an biya Naira miliyan 42,379,100 na tafiye-tafiyen Shugaban kasa da kuma sauran abubuwan da su ka dace.
“A ranar 15 ga Maris, an biya Naira 9,484,310 na tafiye-tafiyen Shugaban kasa da kuma wasu makudan kudade. A daidai wannan ranar, an biya N25,393,490 da kuma N34,185,400 don wannan manufa,” bayanai sun nuna.
“Bugu da kari, gwamnatin ta kashe sama da Naira miliyan 2.9 tsakanin 24 ga watan Fabrairu zuwa 15 ga Maris, 2024, wajen canjin kudaden kasashen waje domin daukar nauyin tafiye-tafiyen da shugaba Bola Tinubu, da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, da uwargidan shugaban kasa Remi Tinubu suka yi.
Tafiyen sun hada da ziyara zuwa Dubai, da Ethiopia, da Switzerland, da Laberiya, da Faransa, da kuma Cote d’Ivoire, tare da wasu makudan kudade da aka yi amfani da su wajen sayen dalar Amurka domin wadannan tafiye-tafiye.
Kudaden da aka kashe sun janyo su ka sosai, musamman ganin yadda hakan ya zo daidai da matsananciyar tabarbarewar tattalin arziki a Najeriya.