
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ci akwashin miƙa mulki ga duk wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Shugaban ya tabbatarwa da ƴan Nijeriya da ƙasashen waje cewa zai yi ƙoƙari a yi sahihin zaɓe da kuma zai tabbatar da ya miƙa mulki ga duk wanda ya lashe zaɓen.
Kakakin shugaban ƙasa, Femi Adesina ne ya baiyana cewa Buharin ya faɗi hakan ne a taron ƙarawa juna sani kan Dimokraɗiyya ta yanar gizo, wanda Shugaban Ƙasar Amurka, Joe Biden ya shirya.
Buhari ya ƙara da cewa gwamnatin sa za ta yi abinda ya dace domin tabbatar da mika mulki cikin lumana.