Home Labarai Dukiya ta miliyoyin Naira ta salwanta yayin da gobara ta ƙone shaguna 3 a Jigawa

Dukiya ta miliyoyin Naira ta salwanta yayin da gobara ta ƙone shaguna 3 a Jigawa

0
Dukiya ta miliyoyin Naira ta salwanta yayin da gobara ta ƙone shaguna 3 a Jigawa

A kalla shaguna uku da wasu kayayyaki na miliyoyin naira ne suka kone a jiya Juma’a sakamakon gobara da ta tashi a unguwar kasuwar Bakin da ke karamar hukumar Hadejia a jihar Jigawa.

DSC Adamu Shehu, kakakin hukumar tsaron farin kaya ta kasa, NSCDC a jihar ne ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na ƙasa afkuwar lamarin a Dutse a yau Asabar.

Shehu ya ce gobarar ta kone kantuna uku da rumfa da wani bangare na wani masallaci a yankin.

“A ranar Juma’a da misalin karfe 10:30 na dare ofishin hukumar NSCDC reshen Hadejia ya samu kiran gaggawa na tashin gobara a rukunin shaguna Na Malam Zangi da ke Bakin Kasuwa, babbar kasuwar Hadejia.

“Nan da nan aka tura tawagar jami’an bayar da agajin gaggawa zuwa wurin domin kashe gobarar tare da ceto dukiyoyin da ba su kone ba tare da kiyaye sata.

“Abin takaici, a lokacin da suka iso, gobarar ta riga ta cinye wayoyi uku da shagunan na’urori, rumfa da wani bangare na wani masallaci,” in ji Mista Shehu.

Ya bayyana cewa har yanzu ba a gano takamammen sanadiyyar da wutar ta tashi ba.

Ya kara da cewa babu wanda wutar ta rauanata ko ta kashe.