Home Labarai DUNIYA INA ZA KI DA MU: An sace ragon layyar liman a Plateau

DUNIYA INA ZA KI DA MU: An sace ragon layyar liman a Plateau

0
DUNIYA INA ZA KI DA MU: An sace ragon layyar liman a Plateau

Ragon layyar limamin masallacin Juma’a na unguwar Mista Ali a karamar hukumar Bassa ta jihar Plateau, Imam Abdulkadir ya yi ɓatan dabo a jajibirin Babbar Sallah.

Rahotanni sun ce an sace ragon Malam Abdulkadir ne a lokacin da aka yi ruwan sama a yankin a jajibirin Sallah.

Wani Limamin masallacin idin, Haruna Yaqub ne ya bayyana haka a yayin hudubar bayan sallar idi.

Yaqub wanda ya yi Allah wadai da lamarin, ya bayyana shi a matsayin “rashin imani”.

Ya kara da cewa hakan ya nuna cewa mutane ba su da tsoron Allah.