Robert Mugabe

An bayar da sanarwar korar Shugaba Robert Mugabe daga matsayin jagoran jam’iyyar ZANU-PF dake mulkin kasar. Tuni kuma, jam’iyyar ta bayarda sanarwar maye gurbinsa da tsohon mataimakin Shugaban kasa da Mugabe ya kora, Emmerson Mnangagwa. Wakilan jam’iyyar suka bayyanawa kamfanin dillancin labarai na AFP a birnin Harare bayan kammala wani taro.

“Mun cimma yarjejeniya tare da rattaba hannu akan daftarin da ya amince da a kori Shugaba Mugabe daga matsayin jagoran jam’iyyar ZANU-PF tare da maye gurbinsa da tsohon mataimakin Shugaban kasa Mnangagwa a matsayin sabon jagoran jam’iyyar.”