Shugaban 'yan Shiah na Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky

Wasu rahotanni wadan da ba na hukuma ba, naa nuna cewar Shugaban ‘yan Shiah na Najeriya Ibrahim El-Zakzaky na cikin wani mawuyacin hali a inda ake tsare da shi, har ma wasu bayanai da ke yawo a shafukan intanet ke cewa ya mutu. Amma kamar yadda wani jami’i ya tabbatarwa da PRNigera Zakzaky na nan lafiya.

“Jita jitar cewar ya mutu, aikin wasu marasa son zaman lafiya ne, wanda suke son yin amfani da wannan damar domin kawo haustini da yamusti, musamman a tsakanin magoya bayan Zakzaky.”

A lokacin da yake tattaunawa da PRNigeria a Abuja, wani jami’in tsaron farin kaya ya shaida musu cewar “Kamar yadda nake magana da kai yanzu, Zakzaky da matarsa suna nan cikin koshin lafiya”

“Suna yin irin Sallarsu a cikin yanayin da ake kula da su”

“Wadan da suke yayata cewar ya mutu,sam basa nufin kasarnan da alheri, masu son kawo husuma ne kawai”

“Muna tabbatar maka cewar Zakzaky da mai dakinsa suna hannun jami’an tsaro cikin koshin lafiya”

“A sabida haka labarin da ake yadawa cewar ya mutu, kanzon kurege ne ba shi da tushe balle makama”