Sheikh Aliyu Said Gamawa
 Kayi riko da imani da kokarin neman ilimin addini da yawan ibada hakan zai sa ka rayu cikin yardar Allah.
-Kafin kayi rubutu kayi nazari akai, kuma kafin kayi magana kayi tunani akai, yin tunanin zai raba ka da yin abin dana sani a rayuwa..
-Duk abin da ya faru da kai kafin ka yanke hukunci kayi bincike akai, kuma duk abinda ya faru kayi hakuri da  tawakkali, duk halin da ka samu kanka a ciki ka dogaro ga Allah.
-Ka natsu sosai yayin mu’amana da mutane, ka saurarai mai zuwa maga da magana ka sani ba kowacce magana ake yarda da ita ba..Don ba kowa ne mai baka shawara ne ke nufin ka da alheri ba..
In an kawo maka labari kada kayi farat ka musanta, ka sauraro alamar cikar hankali ne, Tabbas ba kowacce magana ake karyatawa ba zai yiwu ka samu mafita cikin maganar da ake kawo maka..
– Ka kame harshen ka daga kushe mutane, kullum ka zamo cikin masu fadin alheri akan mutane, Musulmi na kwarai yana kiyaye umarnin “Fadi Alkairi ko kayi shiru”..
– Yi nazari ka dubi rayuwar ka da kyau, abin fata shine Ka yawaita aikata Alkairi fiye da sharri, haka nan kafi yawaita fadin gaskiya..
– Ka nisanci hassada da aibata mutane, Ka yawaita kyakyawar addu’a da fata akan ka da mutane fiye da mummuna..
– Kana yiwa mutane zaton alheri, ka yi hakuri ka zauna da kowa da halin sa, ka sani ba kowa bane mutumin kirki, hakanan ba kowa bane mutumin banza..
-Ka nisanci mummunar dabi’ar yawan zagi, tabbas yawan ashar da zage-zage alama ce ta ashararanci da rashin nagarta. Ka rike mutumcin ka kada kana zagin kowa, kuma in an zage ka kayi hakuri ka yafe, ka sani zagin zai koma kan wanda ya zage ka.
– Ka zamo mai godiya da yabawa wanda duk yayi maka alheri komi nisan lokaci. Hakika manta alheri da butulcewa mutane shukawa kai sharri ne kuma aikin marasa imani ne..
-Ka kyautata zato ga Allah, kuma kafin ka roki wani abu gun Allah ka yi masa godiya akan abinda kake dashi, ka sani rai da lafiya ma arziki ne. Yawan korafi da koke-koke alamar rashin godiya ne da butulci ga Allah..
– Ka sani duk dan adama ajizi ne, don haka Ka yawaita neman gafara a gun Allah dare da rana, kuma kar ka cuci kowa don ranar lahira da aikin ka na alheri za’a biya duk wanda ka aibata ko ka cutar dashi anan duniya.
– Ka rike kaunar Annabi Muhammad (saw) safiya da maraice tabbas  yawaita salati ga  Annabi (saw) yana samar da lada mai yawa da kara imani, Ka sani ya kai dan uwa wallahi baka da kamar Annabi Muhammad (saw)..
– Kada kana fifita bin tafarkin shaidan fiye da hanyar Allah a bayyane da 6oye cikin harkokin ka na yau da kullum. Ka sani akwai mala’iku tare da kai masu rubuta aiyukan ka dare da rana..
– Wajen mua’amalar ka da Iyaye, dangi na zumunta, abokai, Iyalanka Kada kayi yaudara da yi masu karya ka sani za’a yi hisabi a tsakanin ku..
– Yayin neman aure da zama da iyali kada ka tozarta soyayya, ka kaunaci mai sonka don Allah. Ka guji yin sanadib zubar hawayen masoyi, a rayuwa duk abinda kayi Kaima wata rana za’ayi maka ko ayi maka wanda ya fishi…
– Idan ka ga mai mummunar tarbiya, ko mai aikata laifi Kada kayi saurin la’antarsa abin so shine kayi masa addu’a ta neman shiriya kuma kayi shiru…
– Idan kaga mabukaci da mai rauni kayi godiya ga Allah kuma ka hanzarta yi masa agaji, da amsa bukatar sa, in ka taimakeshi tabbas Allah zai biyaka…
– Yi kokari ka yawaita sadaka da kyauta saboda suna kankare zunubai da karawa rayuwa albarka..
– Ka taimaki tsoho da tsohuwa, da duk mabukaci koda ba ‘yan uwanka bane kaima wata rana za’a taimake ka ko a taimaki naka…
– Ka sada zamunci domin yana kara nisan kwana kuma yana kara Arziki, yanke Zumunta yana shafe albarkar rayuwa da jawo matsaloli da masifu iri-iri mu fadaka…
Tsayawa bukatar mutane aikin Salihan bayi ne, yi kokari ka zama mai yawan alheri da tsayawa duk mai bukatar taimakon ka…
– Ka nisanci dabi’ar rowa da matsin hannu da kankamo don zasu jawo fushin Allah akan ka, da  shafewar albarka ga rayuwar ka, sannan Allah zai sa mutane zasu tsane ka, kuma tsatson ka suyi gadon ka, kuma za’a ana mummunan shaida da ambato akan ka kana raye da bayan ka mutu. Da yawan masu nauyin hannu na rashin saka alheri basa yin kyak-kyawar karshe..
-Ka da Ka raina mutane ko kana kyamar su don wata ni’ima da aka yi maka.  Wanda aka bashi ilimi, mulki, dukiya, da hikima ya godewa Allah. Ka sani Allah ya na son bayinsa in ka tozarta ko ka wulakanta su zai saka masu…
Allah ya kawo mana dauki ya kuma sa mu dace duniya da lahira, Amin.