Shugaban kasa Muhammadu Buhari

A lokacin da take mayar da martini kan irin yadda aka dinga sukar sabbin naɗe naɗen da akai na Shugabannin Hukumomin gwamnati, inda aka samu matattu cikin jerin sunayan mutum 1,468 da aka baiwa muƙamai, fadar Shugaban ƙasar tace babu wani abin zargi kan jerin sunayan, domin sunayan ba tun yanzu aka tsara su ba.

Fitattun waɗan da aka kalubalanci nadin nasu, sun hada da Sanata Francis Okpozo, wanda ya mutu a shekarar 2016, kuma aka bayar har da sunansa a jerin sabbin sunayan da aka fitar ranar Juma’a a matsayin Shugaban hukumar Nigerian Press Council.

Mista Okpozo tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin rusasshiyar jihar Bendel ne, ya mutu a birnin Benin bayan wata gajeruwar rashin lafiya, haka kuma, an taba zabensa a matsayin Sanata a karkashin rusasshiyar jam’iyyar SDP.

Bayan haka kuma, mai Magana da yawun fadar Shugaban kasa, Malam Garba Shehu yayi bayanin cewar, wadannan jerin sunaye an tsara su ne tun lokacin tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya wanda aka sallama daga aiki bayan da aka zarge shi da yin sama da fadi, Babchir David Lawal.

Ya kara da cewar, abinda ya faru shi ne, an umarci sabon sakataren gwamnati da ya cigaba daga inda BD Lawal ya tsaya kan tsara sunayen mutanan da za’a baiwa mukaman, ya kuma fitar da sunayen ba tare da ya bisu daki daki ba kamar yadda aka bashi umarni.

A lokacin da yake tattaunawa ta wayar tarho da wakilin jaridar PREMIUM TIMES, mai Magana da yawun fadar Shugaban kasa, Garba Shehu ya cigaba da cewa, “A shekarar 2015 Shugaban kasa ya umarci dukkan Shugabannin jam’iyyar APC da su mika masa sunnayen mutane 50 da za’a nada su a wadannan mukamai”

“A sabida haka, an gama tattara wadannan sunayan ne a babbar sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa, daga nan aka mika sunayen zuwa ga ofishin sakataren Gwamnatin tarayya na lokacin Babachir David Lawal”

“Haka kuma, an samu korafi daga wasu Gwamnonin jam’iyyar APC, wanda suke jin anyi musu ba daidai ba wajen tsallake su a nemi jam’iyya da ta bayar da sunayen, a sabida haka domin baiwa Gwamnonin dama suma, Shugaban kasa ya kafa kwamiti karkashin mataimakinsa, domin ya duba korafin Gwamnonin kuma yaga abinda za’a iya yi akai”

Malam Garba Shehu ya kara da cewar, an jinkirta aikin kwamatin mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ne, sabida a daidai lokacin Shugaban kasa ya kamu da rashin lafiya.

“Tafiyar Shugaban kasa jinya, ya sa aka samu tsaiko kan batun tantance sunayen wadan da ya kamata a baiwa mukaman, ba kuma yin maganar jerin sunayen ba, har sai da Shugaban kasa ya bukaci da a kuma kawo masa sunayen a yanzu”

Malam Garba Shehu bayyana cewar lallai an tafka abin kunya a wannan jerin sunaye, sai dai yace, babu wani dan Adam ajizi ne, babu wanda ya gagari yayi kuskure.

A sabida haka, wannan kuskuren da aka samu a wadannan jerin sunayen ba zai taba zama abin zargin na cewa an shirya rashin gaskiya kan lamarin ba. Haka kuma, yace dukkan kurakuran da aka yi a jerin sunayen za;a gyara su.