
Israa Jaabis na daga cikin Falasɗinawa mata da aka saki daga gidajen yarin Isra’ila ranar Asabar, a wani ɓangare na musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Hamas.
An ɗaure ta a gidan yarin tun shekarar 2015, bayan da motarta ta lalace a kan wata babbar hanya, kilomita ɗaya da rabi daga wani shingen bincike a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
An samu gardama kan dalilin lalacewar motar, Inda Isra’ila ta ce matar ta yi yunƙurin kai harin bom ne da motar.
To amma a lokacin kafofin yaɗa labaran Larabawa sun ce motar ta lalace ne sakamakon samun matsalar inji, lamarin da ya sa motar ta kama da wuta.
Jaabis ta samu raunukan ƙuna a lokacin aukuwar lamarin, inda har fuskarta ta ƙone.
Daga nan ne aka yanke mata hukuncin ɗaurin shekara 11 a gidan yari, inda kawo yanzu ta shafe shekara takwas daga ciki, kafin a sake ta a jiya.
A shekarar da ta gabata ne ta rubuta takardar buƙata da hukumomin gidajen yarin Isra’ila na ba ta damar, yi mata aiki a hancinta da kuma fuskarta, buƙatar da Isra’ila ta yi watsi da ita.
Bayan da ta shaƙi iskar ‘yanci, Jaabis, mai shekara 38 ta rungume ɗanta, Mua’tassim, mai shekara 15, da ta bari a lokacin yana ɗan shekara takwas a duniya.