Home Labarai FALLASA: An gano wani kantin ƴan China da aka hana ƴan Nijeriya yin siyaiya a Abuja

FALLASA: An gano wani kantin ƴan China da aka hana ƴan Nijeriya yin siyaiya a Abuja

0
FALLASA: An gano wani kantin ƴan China da aka hana ƴan Nijeriya yin siyaiya a Abuja

An gano wani babban kanti na yan kasar China dake babban birnin tarayya Abuja, da ke hana ƴan Najeriya su yi siyayya, kamar yadda binciken da PUNCH Online ta gudanar ya nuna.

Babban kantin da ke cibiyar kasuwanci ta China, dake kan titin Umaru Musa Yar’adua a Abuja, ya yi shura wajen sayar da kayan abinci da abin sha na kasar China.

A lokacin da wakilin PUNCH ya ziyarci babban kantin domin tabbatar da sahihancin wannan zargi a ranar Lahadi, jami’an tsaro da ke kofar kantin sun tabbatar da cewa jami’an kantin sun ba da umarnin ne a farkon wannan shekara ba tare da bayyana dalilai ba.

Ɗaya daga cikin masu gadin, wanda babu sunansa a jikin kakin sa kuma ya ki bayyana sunansa, ya ce ana hana masu siyaiya wadanda ba ƴan China ba shiga kantin tun daga bakin kofa kamar yadda shugabancin wajen ya umarta.

Mai gadin ya ce, “A yanzu haka, shugabannin wajen nan sun dakatar da komai. Gaskiya suna sayarwa, amma sun ce mutanenmu su daina zuwa. Sun ce mutanen kasar China ne kawai aka ba su damar yin siyayya a nan. Shagon an yi shi ne don mutanen China kawai. An ba wa mutane izinin shigowa a shekarar da ta gabata, amma tun daga watan Janairun bana, sun canza doka, sun ba da umarnin cewa ba wani dan Najeriya da zai sake shiga.

“Ba a sanar da mu wani dalili na manufar ba, amma mun gaya musu cewa su cire duk wani tallace-tallace daga Intanet domin mutane su daina zuwa.”

Sai dai masu gadin sun bar wakilin PUNCH din ya shiga, saboda a cewar jami’in, “Yau Lahadi ne, kuma babbar rana ce.”

A lokacin da wakilin PUNCH ya nemi jin ta bakin babban manajan kantin domin jin karin bayani a hukumance, jami’an tsaro da ma’aikatan kantin sun ki bayar da lambar wayar da saboda fargabar faɗa ko kora.