29.1 C
Abuja
Tuesday, June 6, 2023

An fara makokin kwanaki 3 bisa mutuwar Pele a Brazil

Must read

Al’ummar Brazil sun fara makokin kwanaki 3 game da mutuwar tauraron kwallon Duniya Pele da ya mutu a jiya alhamis ya na da shekaru 82 bayan fama da cutuka daban-daban ciki har da cancer da kuma ciwon koda.

Jim kadan bayan sanar da mutuwar Pele ne shugaba Jair Bolsonaro ya sanar da hutun kwanaki 3 domin makokin dan wasan wanda ya daukaka darajar Brazil a idon duniya.

Shugaba Bolsonaro da ke shirin ban kwana da mulki a karshen makon nan, ya bayyana Pele a matsayin nasarar Brazil wanda duniya bazata taba mantawa da gudunmawarsa wajen hada kan jama’a ba.

Ɗiyar Pele, Kele Nascimento da ke bayar da bayani kan halin da ya ke ciki ga magoya baya, a yammacin jiya Alhamis ta wallafa hoton bidiyon da ke nuna mahaifin nata na ban kwana sa’o’i ƙalilan gabanin mutuwarsa.

Yayinda ta sake wallafa wani hoto da ke nuna hannunta akan cikinsa ita kuma ta kwantar da kanta a gefen gadon da ya ke kwance, tare da rubuta ‘‘Ba abin da za mu iya yi maka sai godiya muna matukar kaunarka, kwantawarka lafiya’’, kalaman da ke nuna mutuwarsa.

Asibitin da Pele ya kwanta na Albert Einstein da ke Sao Paulo ya tabbatar da cewa zakaran kwallon na Duniya ya mutu ne sakamakon dakatawar aikin wasu sassa a cikinsa.

A tsawon shekaru 21 da ya shafe ya na taka leda, Pele ya zura kwallaye dubu 1 da 281 a wasanni dubu 1 da 363 ciki har da kwallaye 77 da ya zurawa kasarsa a wasanni 92 da ya doka mata.

More articles

Latest article

X whatsapp