
Malcolm Oseahon, kwararre a kan harkar fasahar zamani, ya baiyana cewa fasahar zamani, ICT, na ɗaya daga cikin turakun ci gaba da shugaba Bola Ahmed Tinubu zai rike domin ya samu nasara a mulkinsa.
Oseahon ya yi magana game da kiraye-kirayen da ake ta yi na rusa Ma’aikatar Agaji da Rage Talauci ta Tarayya (FMHAPA) yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise TV.
Ya ce ma’aikatar za ta iya cika aikinta idan aka mai da ita ƙarƙashin wata ma’aikatar, ba wai mai aiwatarwa ko zartaswa ba.
Oseahon ya bayyana cewa, kamata ya yi ma’aikatar tare da taimakon ICT ta mayar da hankali kawai wajen daidaitawa, sa ido, da daidaita ayyukan gwamnati a fadin kananan hukumomi 747, jihohi 36, da babban birnin tarayya Abuja, maimakon tsoma baki a harkokin kudi da aiwatar da ayyuka, in dai ba bisa wata larura ba.
Oseahon, wanda ya samu horo a kasar Koriya, ya bayyana yadda amfani da fasahar zamani a aiyukan gwamnatin, inda ya ce hakan zai haifar da gudanar da aiyuka cikin inganci da amana.
Dole ne gwamnati ta nemo hanyar da za ta kasance a cikin rayuwar wadannan mutane a kullum, don samun damar fitar da su a zahiri daga kangin talauci, kuma ICT a matsayin mai ba da damar hidimar gwamnati ita ce hanya daya tilo kuma mafita.