
Gobara ta ƙone makwancin ɗalibai mata, sakamakon fashewar tukunyar gas a jami’ar jihar Yobe da ke Damaturu.
Daily Trust ta jiyo cewa wutar ta tashi ne da misalin karfe 7 na yamma a jiya Talata sakamakon fashewar tukunyar gas a ginin dakunan.
An jiyo cewa an kwantar da ɗalibai takwas sakamakon ɗimaucewa a asibitin jami’ar da babban asibitin Damaturu, sai dai kuma rahotanni sun baiyana cewa ba a samu rasa rai a gobarar ba.
Hukumar jami’ar ta tabbatar da gobarar, inda ta ce ta faru ne a sabon ginin makwancin ɗalibai mata.
Abdulmumini Kolo Gulani, wanda ya fitar da sanarwar, ya ce ma’aikatan kashe gobara na jami’ar ne su ka samu nasarar kashe wutar.
Ya tabbatar da cewa an kwashe dukkan ɗaliban sashin lafiya lau.