Home Labarai Ƴan fashin daji sun hallaka tsohon ɗan takarar gwamnan Zamfara a titin Kaduna-Abuja

Ƴan fashin daji sun hallaka tsohon ɗan takarar gwamnan Zamfara a titin Kaduna-Abuja

0
Ƴan fashin daji sun hallaka tsohon ɗan takarar gwamnan Zamfara a titin Kaduna-Abuja

 

Ƴan fashin daji sun kashe tsohon ɗan takarar gwamna a Jihar Zamfara, Sagir Hamidu a kan titin Kaduna-Abuja.

Marigayin, wanda shine mamallakin FAMAKS British Schools a Abuja da Kaduna, ya tsaya takarar gwamna ne a jam’iyar APC.

Maharan sun harbe shi ne har lahira lokacin da su ka buɗe wuta a kan matafiya a Rijana da misalin ƙarfe 4 na yamma a yau Lahadi.

Wata majiya daga jami’an tsaro ta baiyanawa DAILY NIGERIAN cewa marigayin na ɗaya da ga cikin waɗanda harsashin da ƴan ta’addan su ka riƙa harbawa ya samu.