
A jiya Talata ne aka gurfanar da wani Fasto na Cocin Redeemed Christian Church of God, RCCG, Emmanuel Orekoya a gaban kotun hukunta laifukan fyaɗe da rikicin cikin gida da ke Ikeja bisa zarginsa da yi wa diyarsa mai shekara 17 fyade ya kuma yi mata ciki.
Wanda ake tuhumar na fuskantar tuhume-tuhume biyu da suka hada da jima’i na haram da kuma fyaɗe bayan da gwamnatin Legas ta shigar da shi ƙara.
Lauyan masu shigar da kara na jihar, Misis Abimbola Abolade, ta shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a wani lokaci a 2017 a titin Jacob Adeleye, Odoeran, a yankin Itire na jihar.
Mai gabatar da karar ta kuma shaida wa kotun cewa Orekoya ya yi lalata da ƴar ta sa har ya shigar da yatsansa a cikin farjinta tare da sanya azzakarinsa a cikin bakinta.
A cewar mai gabatar da kara, laifukan da Orekoya ya aikata sun saɓawa sashe na 137 na dokar laifuka ta jihar Legas ta 2015.
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi.
Mai shari’a, Soladoye ya dage sauraren karar har zuwa ranar 17 ga Afrilu, 2024, domin ci gaba da sauraron shari’ar.