Home Labarai Na fice daga APC ne saboda ba ta tausayin talaka — Doguwa

Na fice daga APC ne saboda ba ta tausayin talaka — Doguwa

0
Na fice daga APC ne saboda ba ta tausayin talaka — Doguwa

Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa, tsohon Sanata a jihar Kano ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar APC.

Doguwa, a wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis ya ce da shi da magoya bayan sa, abokaina ƴan uwa duk sun fice daga APC.

A sanarwar, wacce ya sanya wa hannu a juya Alhamis da yamma, Doguwa ya ce a matsayinsa na gogaggen ɗan siyasa a Kano, amma jam’iyyar APC ta maida shi saniyar-ware.

“Duk wasu shawarwari da kwarewa da muke da su ba a amfani da su ba kuka a neman su daga wajen mu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa “bayan duba na tsanaki da na yi wa jam’iyyar APC, sai na fahimci cewa mafi yawan manufofinta ba na tausayin talaka ba ne, kuma hakan ya saɓa da tarbiyyar siyasar mu,”

Sanata Doguwa ya baiyana cewa bayan shawarwari da tuntuba, “mun ga cewa komawar mu PDP, inda muka baro shi ya fi mana a’ala,” in ji shi