Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana ficewar tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar a matsayin abin kaduwa kwarai da gaske. A ranar Juma’ar nan ne dai Atiku Abubakar ya aikewa da uwar jam’iyyar APC ta kasa wasikar ficewarsa daga jam’iyyar.

Shugaba Buhari ya jajantawa Shugaban jam’iyyar APC na kasa Cif John Oyegun bisa wawar asarar Atiku Abubakar da jam’iyyar ta yi. Buhari ya bayyana Atiku Abubakar da cewar mutum mai matukar muhimmanci a cikin jam’iyyar ta APC.

Shugaban ya bayyana haka ne, ranar litinin a Abuja yayin da yake kaddamar da kwamitin da zasu duba yiwuwar samar da mafi karancin albashi, tare da duba hali da yana yin da ma’aikata suke ciki.

A yayin wannan taron, lokacin da Shugaban ke mika gaisuwa zuwa ga mahalarta taron, da ya zo kan Shugaban APC na kasa, wanda yake wajen, Buhari ya jajanta masa bisa wawar asarar da jam’iyyar ta yi na hazikin mutum, dukda cewar Shugaba Buhari bai ambaci sunan Atiku Abubakar ba, amma dukkan alamu kalamansa na nuni da ficewar Atiku Abubakar daga jam’iyyar.