Lokacin wasan Najeriya da Argentina, inda Maradona ya dagawa 'yan Najeriya yatsan tsakiya alamun mummunan zagi

Hassan Y.A. Malik

FIFA ta yi alwashin daina biyan tsohon dan wasan kwallon kafa na Argentina, Diego Maradona a matsayin jakadanta na kwallon kafa na duniya.

Wannan na zuwa bayan da Maradona ya gaza kimtsa kansa a wasan da kasarsa ta buga da Super eagles ta Nijeriya a ranar Talatar da ta gabata, inda kasarsa ta samu nasara da kyar a kan Super Eagles da ci 2 da 1.

Maradona ya yi murnar zura kwallon Marcos Rojo ta hanyar nunawa magoya bayan Nijeriya dan yatsansa na tsakiya (alamar zagi).

FIFA ta bayyana wannan dabi’a ta Maradona a matsayin abin takaici da rashin nuna kamun kai, inda har ta dauki matakin daina biyansa fam 10,000 da take biyansa a matsayin jakadanta kamar yadda mujallar OwnGoal ta rawaito.

Haka kuma, Maradona ya ki bin umarnin likitocinsa inda suka hana shi kallon karshen wasan domin kare lafiyarsa. Amma sai ya yi kunnen uwar shegu da umarnin na likitoci, dalilin da ya sa ya jefa kansa da kansa cikin haɗarin lafiya

FIFA ta ja kunnen Maradona da ya nutsu ya kuma zama mai kimtsi a ragowar wasannin da kasarsa ta Argentina za ta buga a gasar.
Akwai yiwuwar FIFA ta hana masa sake shiga kallon wasanni in har ya sake maimaita irin abinda ya yi a wasan Nijeriya.