Categories
Labarai

Fitaccen dan jarida Mahmoon Baba-Ahmed ya kwanta dama

Allah ya yiwa fiaccen dan jarida, Marubuci Alhaji Mahmoon Baba-Ahmed rasuwa yana mai shekaru 74 a duniya.

Mahmoon Baba Ahmed ya rasu sakamakon wata ‘yar gajeruwar rashin lafiya, a cewar dansa Aminu a lokacin da yake shaidawa DAILY NIGERIAN.

Alhaji Mahmoon ya fara aikin jarida ne a matsayin mai gabatar da labarai a kamfanin yada labarai na Arewacin najeriya mai suna BCNN a shekarar 1971.

Daga bisani Alhaji Mahmoon ya fara aiki da kamfanin buga jaridu na Arewa NNN a matsayin mataimakin Edita kafin daga baya ya koma BCNN.

Yayi aiki a matsayin mai aiko da rahoto daga jihohin Kaduna da Kano da Bauchi da Borno da Filato da kuma Legas ga Gidan radiyon tarayya na Kaduna.

Daga nan kuma aka nada shi a matsayin babban Daraktan yada labarai na ma’aikatar yada labarai ta jihar Kaduna

A shekarar 1983, Gwamnan jihar Kano Alhaji Sabo Bakinzuwo, ya nada shi a matsayin Janar Manaja a gidan Radiyon jihar Kano. Mahmoon yayi shekara daya a Radiyon Kano kafin daga baya ya koma gidan Radiyon tarayya dake Kaduna.

Alhaji Mahmoon Baba Ahmed ya kasance dan jarida mai zaman kansa bayan da yayi ritaya daga aikin jarida,sannan yana gabatar da mukala duk sati a jaridar Aminya da kuma jaridar Blue Print.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *