Home Labarai Fursunoni 3,590 ne ke fuskantar hukuncin kisa a Nijeriya — NCoS

Fursunoni 3,590 ne ke fuskantar hukuncin kisa a Nijeriya — NCoS

0
Fursunoni 3,590 ne ke fuskantar hukuncin kisa a Nijeriya — NCoS

Akalla fursunoni 3,590 ne a duk cibiyoyin da ake tsare da su a Najeriya ke fuskantar hukuncin kisa, in ji Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa, NCoS.

Jami’in Hulda da Jama’a na NCoS, Abubakar Umar ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a yau Laraba a Abuja.

Umar ya ce adadin fursunonin da ake tsare da su a cibiyoyi a fadin kasar sun kai 84,741 wadanda suka kunshi maza 82,821 da kuma mata 1,920 “kamar yadda a ranar 3 ga Satumba, 2024.

Kakakin NCoS din ya ce jimillar fursunonin da ke jiran shari’a, ATIs, sun kai 57,750 da suka kunshi maza 56,303 da mata 1,447.

“fursunoni da aka yanke wa hukunci 21,900 ne da suka hada da maza 21,519 da mata 381, yayin da masu daurin rai-da-rai 1,501 suka kunshi maza 1,478 da mata 23.

“Jimillar adadin fursunonin da ke kira kisa (IDR) sun kasance maza 3,517 da mata 73 wanda jimlar su ya zama 3,590,” in ji shi.

Umar ya ce galibin fursunonin da ake tsare da su na jiran shari’a ne, ATPs, wanda ke zama babban kalubale ga Hukumar saboda yawan su.