A shekarar 1997 a birnin Frankfut na kasar Jamus, wani mutum ya shaidawa ‘yan sanda cewar an sace masa mota, domin a inda yake zaton ya ajiye ta ya duba be ganta ba.

Bayan shekaru da aka nemi motar a inda ake zaton an ajiye ta ba’a ganta ba, hukumomi a birnin suna ta bibiya domin gano wanda ya sace motar, sai daga bisani ne aka gano cewar, wannan motar, ita ya mance ainihin inda ya ajiye ta ne shekaru 20da suka wuce, dan haka yayi zargin ko an sace ta.

Yanzu haka dai,an gano motar a wani shagon ajiye motoci na wani tsohon kamfani, wanda ake gab da ruguje shi, kanan aka gano shi.

Jaridar Independent ta Ingila ta ruwaito labarin.