Home Labarai Harin bam din Kaduna: Mun ɗauki darasi kuma za mu ƙara lura wajen ayyukan mu — Shelkwatar Tsaro

Harin bam din Kaduna: Mun ɗauki darasi kuma za mu ƙara lura wajen ayyukan mu — Shelkwatar Tsaro

0
Harin bam din Kaduna: Mun ɗauki darasi kuma za mu ƙara lura wajen ayyukan mu — Shelkwatar Tsaro

Rundunar sojin Najeriya ta sake bayyana nadamar ta a kan harin da jiragen yaki marasa matuki suka kai a kauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.

“Mun ɗauki darasi kuma za mu inganta ayyukanmu”, Daraktan Ayyukan Harkokin Watsa Labarai na Tsaro, Maj.-Gen. Edward Buba, ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Alhamis a Abuja.

Buba ya bayar da tabbacin cewa sojojin Najeriya za su ci gaba da gudanar da ayyukansu daidai da dokokin kasa da kasa da ka’idojin aiki.

Yayin da ya yi watsi da rade-radin cewa rashin hadin kai tsakanin jami’an sojin ne ya haifar da matsalar, Buba ya ce tare ake gudanar da ayyukan soji a fadin kasar da sojoji na ruwa da na sama da na kasa.

“A kan lamarin da ya faru, ina tabbatar muku cewa sojoji sun dauki darasi kan abubuwan da suka faru kuma za su ci gaba da yin gyare-gyare yayin da muke gudanar da ayyukan mu.

“Wani lamari ne da ya faru kuma kamar yadda na ambata a takaice, mun kuduri aniyar shawo kan lamarin da yin abinda aya dace,” in ji shi