Home Wasanni Gasar Firimiya: Arsenal ta sha kashi a hannun Everton 2-1

Gasar Firimiya: Arsenal ta sha kashi a hannun Everton 2-1

0
Gasar Firimiya: Arsenal ta sha kashi a hannun Everton 2-1

 

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton ta doke Arsenal 2-1 a wasannin gasar firimiya mako na 15.

Arsenal ce ta fara jefa ƙwallo a ragar Everton a filin wasa na Goodison Park ta hannun Ordegard.

Da ga bisani sai Richarlison ya farke amma alƙalin wasa ya soke ƙwallon sa ka makon ya yi star gida.

Hakan bai kashewa Richarlison gwiwa ba, inda ya ƙara zura wata kwallon a ragar Arsenal amma sai alƙalin wasa ya sake soke ƙwallon.

Da ga bisani ne dai Everton ta samu ta farke ƙwallo ta hannun Richarlison.

A wajen minti na 92 sai Gray ya ƙara, in da a ka tashi 2-1., kuma nasarar Everton ɗin ta sakko da Arsenal zuwa matsayi na 7 ankan teburin gasar, a ƙasan Manchester United