Home Labarai Gobara ta hallaka yara 2 a sansanin ƴan gudun hijira a Borno

Gobara ta hallaka yara 2 a sansanin ƴan gudun hijira a Borno

0
Gobara ta hallaka yara 2 a sansanin ƴan gudun hijira a Borno

Akalla yara biyu ne rahotanni suka ce sun mutu bayan da gobara ta kama ɗaruruwan tantunan ƴan gudun hijira a karamar hukumar Mafa da ke jihar Borno.

An bayyana cewa gobarar ta tashi ne da karfe 11:15 na safe a sansanin ‘yan gudun hijira na Muna Allamdari da ke Maiduguri.

Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar, Dokta Barkindo Saidu, ya ce tawagarsa tare da ‘yan kwana-kwana sun yi kokarin kashe gobarar.

Ya ce yara biyu ne suka rasa rayukansu, bayan da daruruwan tantuna suka kone sakamakon gobarar.

“Mun rasa yara biyu sakamakon barkewar gobara kuma muna kokarin tallafawa ‘yan gudun hijirar yanzu,” in ji Dokta Barkindo.

Wakilinmu ya ruwaito cewa ana kokarin kashe gobarar amma har yanzu ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba.