Home Labarai Gobara ta kone gidan karamar ministar birnin taraiya, Mariya Bunkure a Abuja

Gobara ta kone gidan karamar ministar birnin taraiya, Mariya Bunkure a Abuja

0
Gobara ta kone gidan karamar ministar birnin taraiya, Mariya Bunkure a Abuja

Gobara ta kone gidan karamar ministar babban birnin tarayya, Abuja, Dr Mariya Mahmoud Bunkure da ke Abuja a jiya Lahadi.

Mai taimakawa ministar kan harkokin yada labarai, Austine Elemue, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, ya ce hukumomi na binciken musabbabin tashin gobarar.

Ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10:00 na safe a gidan da ke lamba 7, layin Roseline Ukeji, Okoye Street, Asokoro, Abuja.

Da aka tuntubi mukaddashin daraktan hukumar kashe gobara ta babban birnin tarayya Abuja, Amiola Adebayo, ya ce hukumar ta samu rahoton gobarar da karfe 10:30 na safe, inda nan take ta tura ƴan kwana-kwana zuwa wurin.

Adedayo ya ce duk da cewa ba a yi asarar rayuka ba, amma daukacin saman gidan mai dakuna bakwai ya ƙone kurmus.

Ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da ke ciki kamar gadaje, tufafi, takardu, takaddun shaida, kayan ado da na’urorin sanyaya daki, gami da rufin da sauran kayayyaki masu daraja.

Ya ce an samu ikon kashe gobarar da misalin karfe 2:51 na rana, inda ya kara da cewa ana zargin musabbabin gobarar daga wutar lantarki ne a dakin yara.