
Wata gobara da ta tashi da asubar yauTalata ta kone shaguna 34 a kasuwar waya da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe, inda aka ce ta lalata kayayyakin da darajarsu ta kai Naira miliyan 150.
Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a yankin Abashawa da ke kasuwar da misalin karfe 4:00 na asuba, amma daga bisani jami’an kashe gobara suka kashe ta.
Shugaban Kasuwar, Alhaji Malami Ali ya ce, ”Na farka da asuba da wannan ibtila’i bayan da su (‘yan kasuwar) suka yi min waya suka yi min bayani kan lamarin.
“Mun jiyo cewa wannan lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:00 na safe amma sai da aka hada kai da jami’an hukumar kashe gobara da jama’ar unguwar domin kashe wutar da ta tashi.
‘’ Maganar gaskiya babu wanda zai iya gaya maka abin da ya jawo gobarar, domin shagon da wannan gobarar ta tashi ba shi da wutar lantarki sai dai akwai wutar sola.
‘’Ya zuwa yanzu shaguna 34 ne su ka kone da dukiyar da ta haura Naira miliyan 150.
‘’Muna kira ga gwamnati da sauran hukumomi da su kawo mana agaji domin yawancin ‘yan kasuwar nan sun yi asarar dukiyoyinsu.