
Ofisoshi biyar ne su ka ƙone ƙurmus a wata gobara da ta tashi a Jami’ar Kimiya da Fasaha ta Wudil da ke Ƙaramar Hukumar Wudil a Jihar Kano.
Ofisoshin da su ka ƙone ɗin a ɓangaren koyar da ilimin kimiyya ne na jami’ar.
Wannan na ƙunshe a wata sanarwa da Kakakin Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi ya sanyawa hannu a yau Lahadi.
Abdullahi ya baiyana cewa “a kimanin ƙarfe 12:04 na dare a ranar Asabar ne a ka kira wayar ofishin hukumar da ke Wudil a ka sanar da mu cewa gobara ta tashi a wasu ofisoshin jami’ar.
“Muna karɓar rahoton dakarun mu su ka garzaya su ka kuma isa gurin a daidai 12:07 domin kai agaji,” in ji sanarwar.
Abdullahi ya baiyana cewa ofishin biyar duka sun ƙone.
Ya ƙara da cewa tararratsin wutar lantarki ne ya haifar da gobarar.
Ya yi kira ga al’umma da su riƙa yin taka-tsan-tsan da kayan lantarki, musamman ma da a ke tunkarar lokacin sanyi.